Sulaiman Haruna, mai taimakawa Aisha Buhari kan harkokin yada labarai ya karyata rahotannin da ke cewa tana dauke da juna biyu.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi zargin cewa uwargidan shugaban kasar na da juna biyu, bayan da hotunan tahowarta daga kasar Turkiyya suka bayyana a yanar gizo
Wasu kuma sun yi iƙirarin cewa ba ta da lafiya saboda ta bayyana an hango wani ciki, a cikin hotunan.
Sai dai Haruna ya shaida wa BBC cewa ba wai Aisha ba ta da lafiya ba ne, Kuma wai ciki take da shi ba.
A cewarsa, jita-jita ne kuma daga ɓatanci ne waɗanda ba su da ma’ana.
“Zan iya tabbatar muku dari bisa dari cewa uwargidan shugaban kasa ba wai ba ta da lafiya ba ne. kuma ba wai tana da ciki ba ne kamar yadda wasu rahotanni ke ikirari.
“Wasu daga cikin wadannan rahotannin sun fito ne daga masu yin barna wadanda ba su da ma’ana sosai. Kun san, a zamanin yau, mutane na iya yin sauyawa hotuna yanayi na gaskiya.” inji shi.