Maigari na Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi 111, ya dakatar da duk bukukuwan dare a garin Lokoja da dukkan al’ummomin da ke kusa da su har sai an samu wata sanarwa.
An dauki wannan matakin ne sakamakon ayyukan ‘yan daba wanda suke amfani da bukukuwa domin aikata barna ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a babban birnin.
Ya kuma ci gaba da cewa hakan na ci gaba da karfafa rudani da ciki a tsakanin kungiyoyin ‘yan daba masu hamayya inda suke amfani da lokutan bukukuwa da daddare da sauran bukukuwan da ake gudanarwa a Lokoja da kewayenta.
Ayyukan ƙungiyoyin a lardin masarautar a Kabawa, Karaworo da tsoffin al’ummomin kasuwa sun kasance abin damuwa ga sarkin mai daraja ta farko.
A sakamakon haka, masarautar ta umarci mukarrabansa da su aiwatar da umarnin domin dakile yawaitar ayyukan masu laifi.
Sarkin Warkin Wasa na Lokoja, Malam Muhammadu Baba Shata, ya ce an umarci masu fasahar gargajiya da su kasance masu bin doka da kuma aiwatar da umarnin a matsayin sadaukarwa don dawo da zaman lafiya a titunan Lokoja.