Majalisa za ta binciki ayyuka 10,000 da aka yi watsi da su
Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Kamorudeen Lere Oyewumi ya bayyana cewa kawo yanzu majalisar ta gano ayyukan gwamnati sama da 10,000 da aka yi watsi da su a matakai daban-daban a fadin kasar.
Oyewumi ya ce, Majalisar Dokoki ta Tarayya ta amince da gudanar da cikakken bincike kan ayyukan da aka yi watsi da su da nufin farfado da su a inda ya dace domin ci gaban al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dalilin Da Yasa Muka Yiwa Jakadan Najeriya Kiranye-Gwamnatin Tarayya
Sanatan mai wakiltar Osun ta Yamma a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa an gudanar da binciken ne domin gano ci gaban ayyukan da dalilan watsi da su.
Ya ce an tattaro kwararru a fannoni daban-daban domin tantance fa’ida da kuma nawa ne gwamnati mai ci za ta kashe wajen farfado da ayyuka.
Tsohon kwamishinan hukumar kula da ƙidayar jama’a ta NPC, ya kara da cewa ’yan kwangilar da suka yi watsi da ayyukan za a gano su tare da karfafa musu gwiwa su koma wuraren aiki.
Ya kara da cewa duk inda aka samu wanda ya saba wa doka, to za a mika irin wannan mutumin ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin daukar matakin da ya dace.
Sanatan, wanda ya koka da yadda batun watsi da ayyukan ya zama abin damuwa kuma ba za a iya jurewa ba, ya bayyana cewa gwamnati mai ci za ta dauki tsauraran matakai don rage mummunan abin kunya na kasa.
A wani labarin kuma:Tinubu ya sallami dukkanin jakadun Najeriya a wasu ƙasashe – Minista
Shugaba Bola Tinubu ya sallami dukkan jakadun Najeriya – jakadun aiki da wadanda ba na aiki ba – in ji Ministan Ambasada Yusuf Tuggar.
Ministan ya tabbatar da saukewar da aka yi wa dukkanin jakadun a ranar Asabar a cikin wata sanarwa ta mai bada shawara kan harkokin yada labarai Alkasim Abdulkadir ya fitar.