Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Najeriya da ta baiwa ilimi fifiko a matsayin ginshiƙin zaman lafiya
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta sanya ilimi a matsayin mafi fili a duk wani Yunƙuri na samar da zaman lafiya don gina al’adun zaman lafiya mai dorewa a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Cibiyar Watsa Labarai ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIC) suka fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana bukatar gaggawa ga Gwamnatin Najeriya da ta ba da fifiko kan ilimi a matsayin wani makami na karfafa juriya da mutuncin dan Adam.
Wakilin UNESCO a Najeriya Abdourahamane Diallo ya ce idan aka sanya ilimi a cikin ginshikin kudurinmu na samar da zaman lafiya “zai iya karfafawa Ɗalibai da ƙara basirar ilimin da dabi’un da suka wajaba, don zama wakilan zaman lafiya a yankunansu.”
KARANTA NAN:Tinubu bai iya maida Villa daga Abuja zuwa Legas – Shehu Sani
Yayin da ake karfafa gwiwar Gwamnati ta ba da fifiko kan ilimi a kan babban tsarin siyasarta, ana yin kira mai karfi na hada kan masu fada a ji da sauran kungiyoyin farar hula don ciyar da yunkurin kawo ilimi gaba a cibiyoyin samar da zaman lafiya a dukkan matakai.”
A cikin sanarwar, Mista Diallo ya bayyana cewa, “UNESCO ta kafa wani sabon tsari na ilimi don samar da zaman lafiya mai dorewa, inda ilimi ya ba da dama da yawa don magance tushen maganganun batanci da yarfe, da wayar da kan ɗalibai na kowane bangare.
Wakilin UNICEF a Najeriya Cristian Munduate ta yabawa kudurin Najeriya na aiwatar da wani tsari mai taken “Safe School” da kuma samar da wasu hanyoyi don inganta tsaron makarantu da kuma nuna bukatar ci gaba da samun tagomashi wajen tabbatar da ingancin makarantu.
Ta ce, “A wannan muhimmiyar rana, muna tunatar da mu irin nauyin da ya rataya a wuyanmu na kiyaye muhallin ilimi ga kowane yaro, Ilimi muhimmin abu ne na samar da daidaiton jinsi, na ci gaban tattalin arziki, da ci gaban al’umma, abin bakin ciki shi ne har yanzu bai kai ga yawancin yaran Nijeriya ba, Saboda
tashe-tashen hankula sakamakon hare-haren da ake kai wa al’ummomi da makarantu ciki har da sace dalibai”
Ta kara da cewa wadannan kalubalen na da matukar muhimmanci ga ‘yan mata masu tasowa, wanda hakan na iya dakile ci gaban da aka samu a ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya.