Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan Ƴan Najeriya 250 a Habasha
Majalisar dattijai ta matsa kaimi domin gudanar da bincike kan kashe-kashe da daure ‘yan Najeriya sama da 250 a kasar Habasha.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri mai taken, ‘Akwai bukatar a gaggauta bincike kan kashe-kashen da aka yi wa ‘yan Najeriya sama da 250 a kasar Habasha ba bisa ka’ida ba, wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Mwadkwon, dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, mai wakiltar Filato ta Arewa, da Sanata Victor suka dauki nauyi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnan Neja ya jajantawa Masarautar Borgu kan hatsarin jirgin ruwa
Da yake gabatar da kudirin, Mwadkwon ya bukaci majalisar dattijai da ta umurci kwamitocin kasashen waje da su hada kai da gwamnatin tarayya domin kafa kwamitin gaggawa da zai ziyarci jamhuriyar Habasha da nufin binciki abubuwan da ke faruwa ga ‘yan Najeriya a kasashen ketare.
Ya kuma yi kira ga FG da ta gaggauta umurtar ofishin jakadancin kasar Habasha da ya hada kai da tawagar kwamitocin majalisar dattawa kan kasashen waje da kasashen waje domin samar da dawwamammen mafita kan matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Mwadkwon ya ce, “bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ya nuna cewa ‘yan Najeriya na tsare a gidan yari mafi girma na kasar Habasha kuma suna cikin hadari mai tsanani wanda ya bukaci a gaggauta shiga tsakani da kuma yin cikakken bincike kan munanan ayyukan.”
Ya koka da cewa hakan na faruwa duk da kiraye-kirayen hadin kai tsakanin kasashen duniya.
A wani labarin kuma:NSCDC ta horar da Ma’aikatan ta 280 Kan Sarrafa Makamai
Kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC dake babban birnin tarayya Abuja, Olusola Odumosu, ya gargadi jami’an hukumar da su guji ‘korar mutane.
Ya ba da wannan gargadin ne a wajen bikin bude atisayen kwanaki uku na horar da rundunar da ke yaki da makamai na rundunar a Abuja ranar Laraba.