Yanzu haka dai majalisar dattijai a ranar Alhamis ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na ya ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya, Vanguard ta rawaito.
Hakan ya biyo bayan la’akari da lamunin da Kwamitin ya yi a zaman taron majalisar na ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Nemi Amimcewar Majalisa Kan Ciyo Bashin Bankin Duniya
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya tuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen gwamnatinsa, ya mika irin wannan bukata ga majalisar dattawa ta 9 a watan Mayun 2023.
Sai dai majalisar ta 9 ta kasa yin la’akari da bukatar kafin wa’adin ta ya kare a ranar 11 ga watan Yunin 2023.
Tinubu, a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta tun farko yayin zaman majalisar ya bukaci majalisar ta 10 da ta amince da bukatar karbo bashin.
Shugaban, a cikin wasikar, ya bayyana cewa, za a yi amfani da rancen ne wajen bunkasa shirin Safety Net na kasa.
Wasikar ta Tinubu tana cewa: “Don Allah a lura cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da karin lamuni na dala miliyan 800.
“Wannan za a samu shi ne daga Bankin Duniya don shirin Safety Net na kasa.
“Kuna iya lura da cewa manufar ginin ita ce faɗaɗa ɗaukar rahotannin tallafin na Safety Net a tsakanin talakawa da ‘yan Najeriya masu rauni. Wannan zai taimaka musu wajen shawo kan buƙatu na yau da kullun.
“Kuna iya kara lura cewa a karkashin tsarin musayar kudi na tsarin, gwamnatin tarayyar Najeriya za ta mika kudaden Naira 8,000 a kowane wata ga talakawa miliyan 12 da masu karamin karfi.
“Wannan na tsawon watanni shida ne tare da ninka yawan mutane kusan miliyan 60.
“Don tabbatar da amincin tsarin, za a yi musaya ta hanyar zamani kai tsaye zuwa asusun masu cin gajiyar da wallet ɗin wayoyin hannu.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Gurfanar Da Emefiele A Gaban Kotu
Hukumar DSS ta ce ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a gaban kotu.
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun Abuja ta umarci hukumar DSS da ta saki Emefiele ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.