- Majalisar dokokin Oyo ta amince da bukatar gwamna Seyi Makinde na samun ciyo bashin zunzurutun kudi har naira biliyan 50
- Amincewar ta biyo bayan wasikar bukatar da gwamnan ya aikewa majalisar dokokin jihar
- Majalisar dokokin ta amince tare da bayyana sunayen wasu kwamishinoni da gwamnan ya mika mata
Majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da bukatar gwamna Seyi Makinde na samun ciyo bashin zunzurutun kudi har naira biliyan 50 domin bunkasa ayyukan yau da kullum da manyan ayyuka a jihar, Vanguard ta rawaito.
Amincewar ta biyo bayan wasikar bukatar da gwamnan ya aikewa majalisar dokokin jihar wanda kuma kakakin majalisar, Adebo Ogundoyin ya karanta a zauren taron ranar Talata.
KARANTA WANNAN: Kano: Dan Ganduje Ya Yi Rashin Nasara A Kutun Sauraren Kararrakin Zabe
Gwamna Makinde a cikin wasikar ya ce: “Bukatar wani bangare ne na kokarin gwamnati mai ci na samar da kudaden da take kashewa akai-akai wadanda suka hada da albashi da tarurruka, kashe manyan kudade da tallafin kudade daban-daban na kwangila.”
“Sakamakon na tsawon watanni 45 ne a kan kari na kashi 25.1% a kowace shekara. Wannan abu ne da za a sake dubawa daidai da yanayin kasuwar kuɗi.
Yayin da suke tattaunawa kan bukatar, ‘yan majalisar sun amince da ayyuka daban-daban da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a fadin jihar.
Sun ce irin wannan wurin ba makawa don baiwa Gwamnatin Jiha damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kudi musamman ta fuskar kudaden da take kashewa akai-akai.
A halin da ake ciki, majalisar ta amince tare da bayyana sunayen wasu kwamishinoni guda biyu da gwamnan ya mika mata.
Sunayen sune Miss Wasilat Adegoke Adefemi, haifaffen Lanlate da kuma Dokta Oluwaserimi Adewumi Ajetunmobi.
A cewar wasikar da gwamnan ya aikewa majalisar a zaman da kakakin majalisar ya karanta, an dauki mutanen biyu sun cancanci a nada su a matsayin kwamishinonin gwamnatin jihar.
“Don haka ina neman a tantance tare da amincewa da Miss Adegoke Wasilat Adefemi da Dokta Oluwaserimi Adewumi Ajetunmobi a matsayin kwamishinoni.”
Ogundoyin ya ce har yanzu akwai wasu ma’aikatun da har yanzu ba su da kwamishinoni, inda ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta tantance sabbin kwamishinonin da aka nada.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Tsohon Shugaban NNPP na Kasa, Ya Fice daga Jam’iyyar
Yanzu haka dai tsohon shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Ahmed ya fice daga jam’iyyar
Ana dai kallon matakin na tsohon shugaban jam’iyyar a matsayin wani babbar barna ga jam’iyyar da ta fuskanci babban rikici
Abin takaici, mai makon samun cigaba a cikin jam’iyyar ta kara zurfafa cikin rikice-rikice da tada jijiyoyin wuya wanda ya kai ga dakatar da manyan shugabanninta
Farfesa Rufa’i Ahmed, tsohon shugaban jam’iyyar NNPP, ya fice daga jam’iyyar.
Rufa’i, a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja, ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar “bayan tuntubar juna”.