Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi uku a jihar bisa zargin karkatar da kudade, Daily Trust ta rahoto.
An sanar da dakatarwar ne a ranar Talata bayan an zargi shugabannin da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, kamar yadda dokar sayen kayayyakin gwamnatin jihar Kaduna ta shekarar 2016, sashe na 35 karamin sashe na 23 ya tanada.
Kwamitin wucin gadi kan binciken, wanda mamba mai wakiltar yankin Lere ta Gabas, Munirat Sulaiman Tanimu ta jagoranta, ya yi nazari sosai kan harkokin kudi na kananan hukumomi biyar da suka hadar da: Chikun, Kaura, Kagarko, Soba, da Birnin Gwari.
Majalisar ta ba da umarnin gudanar da cikakken binciken ne bayan wani kuduri da aka cimma a ranar 18 ga watan Yuli, 2023.
Tanimu ta bayyana cewa kwamitin ya gayyaci shugabannin da abin ya shafa domin su samar da takardun kudi da suka hada da bayanan banki daga watan Yunin shekarar 2022 zuwa Yuni 2023, asusun ajiya na sashen (DVA), da aka amince da kasafin kudin na 2022 da 2023, jari da kuma kudaden da ake kashewa na yau da kullum na shekaru daban-daban, da jerin kwangilolin da aka bayar da matakan kammala su da dai sauransu.
Bayan nazarin takardun, kwamitin ya gano cewa shugabannin kananan hukumomin Kaura, Kagarko, da Chikun sun saba wa sashe na 48 na dokar gudanar da kananan hukumomi ta shekarar 2018 da sashe na 35 karamin sashe na 25 na dokar sayen kayayyakin gwamnatin jihar Kaduna ta shekarar 2016.
Ta ce wadannan sassan sun zayyana yadda ya dace da kason kasafin kudi da kuma ka’idojin siyan kayayyakin gwamnati na jihar.
Sakamakon haka, kwamitin ya ba da shawarar cewa shugabannin kananan hukumomin uku su bar ofisoshinsu na tsawon watanni shida masu zuwa don ci gaba da gudanar da cikakken bincike.
Haka kuma an umarce su da kada su kasance a sakatariyoyin kananan hukumomi a wannan lokaci kuma su mika ayyukansu ga mataimakan shugabanninsu.
Majalisar ta kuma amince da cewa shugabannin kananan hukumomin Birnin Gwari da Soba ba su taka wata doka ba amma an tsawatar musu kan gazawa wajen sayen kayayyakin gwamnati a kasafin kudin shekarar 2023 da aka amince da su daga ma’aikatar kananan hukumomin kan lokaci.
Da yake bayar da gudunmuwa kan rahoton, kakakin majalisar, Yusuf Liman Dahiru, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya jaddada cewa, ya kamata duk masu rike da mukaman siyasa su guji yin almubazzaranci da dukiyar jama’a, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri a shari’a ba tare da nuna wani fifiko ba.
A wani labarin kuma, Dan Takarar Majalisar Tarayya Na SDP Ya Fice Daga Jam’iyyar, Ya Koma PDP Ya Bayyana Dalili
Gabannin gudanar da zaben gwamnan jihar Imo da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, dan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar SDP, Stanley Onyiriuka, ya fice daga jam’iyyar a karamar hukumar Ohaji Egbema ya koma jam’iyyar PDP.
Hakan ya biyo bayan amincewa daban-daban na dan takarar gwamnan PDP, Sanata Samuel Nnaemeka Anyanwu a matsayin dan takara a zaben watan Nuwamba na daidaikun mutane, kungiyoyi da jam’iyyun siyasa.