Majalisar Ribas ta fara wani yunƙurin tsige Gwamna Fubara
A ranar Asabar ne majalisar dokokin jihar Rivers ta yi barazanar tsige gwamnan jihar, Sim Fubara.
Majalisar ta ce “ba za ta yi jinkirin tsige Fubara ba, idan ta zama mataki na karshe na tabbatar da kundin tsarin mulki.”
KARANTA WANNAN LABARIN:Ista: Ku shiga siyasa gadan-gadan – Kungiyar CAN ga Kiristocin Najeriya
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, Martin Amaewhule ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar.
Shugaban majalisar ya kasance tare da abokan aikinsa 26.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar wakilai 27 da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, suka yi kaca-kaca a tsohuwar Majalisar Yakin Neman Zaben Shugabancin Jam’iyyar PDP na Jihar Ribas, karkashin jagorancin Dr Abiye Sekibo, kan caccakar da ta yi wa Wike kwanan nan.
A shekarar 2023, ‘yan majalisar sun yi barazanar tsige gwamnan ne biyo bayan arangamar da ya yi da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Amma a watan Disamba, ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers 26 sun janye sanarwar tsige Fubara.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar janyewar da aka karanta a zauren majalisar a ranar Laraba.
Sun ce sun yanke hukuncin ne saboda mutunta shugaba Bola Tinubu wanda ya kira taron sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.
DAILY POST ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Fubara da magabacinsa, Wike.
A wani labarin kuma:Ka cika alkawuran da ka yi wa ƴan Najeriya – Bode George ga Tinubu
Wani jigo a jam’iyyar PDP, Bode George, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya cika alkawuran da ya yi wa al’ummar Najeriya.
George ya yi wannan kiran ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a yau Juma’a.