Majalisar Wakilai, a ranar Laraba, ta bukaci hukumar kula da gidaje yari ta Najeriya da ta yi bayani kan fursunonin da suka tsere daga cibiyar tsaro ta Kuje a shekarar 2022.
Majalisar ta umarci kwamitocinta mai kula da cibiyoyi, cikin gida, da na ‘yan sanda da su tuntubi shugabannin hukumomin tsaro da abin ya shafa domin gabatar da cikakken rahoto kan halin da fursunonin da suka tsere suke ciki.
Karanta nanGwamnatin Bauchi Za Ta Samar Da Hanyoyin Zamani Na Tsawon Kilomita 200 A Fadin Jahar
Nan da makwanni shida, kwamitocin za su kai rahoto ga majalisar domin ci gaba da aiwatar da dokar.
Emmanuel Ukpong-Udo, mamba mai wakiltar mazabar Ikono/Ini na jihar Akwa Ibom ne ya dauki nauyin kudirin da ya kai ga cimma matsaya a majalisar.
Kungiyar Islamic State a Yammacin Afirka ta dauki alhakin harin Yuli 2022 a Cibiyar dake Kuje, wanda ya kai ga tserewa da dama daga cikin wadanda ake zargi da zama ‘yan Boko Haram.
Ukpong-Udo, yayin da yake jagorantar muhawarar, ya bayyana cewa, “A ranar 5 ga Yuli, 2022 wani hari da aka kai wani gidan yari da ke Kuje a Abuja, ya sa fursunoni 879, ciki har da ‘yan ta’addan Boko Haram 64, suka gudu, 422 da suka rage ba a gano su ba, ko kuma jami’an tsaro suka kama su.
A wani labarin kumaGwamna Bauchi Ya Karbi Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Yi Alkawarin Bashi Hadin Kai
Majalisar ta kuma yi nuni da cewa hukumar da ke kula gidajen yari a Najeriya na bukatar cikakken rahoto kan fursunonin da hanyoyin gano fursunonin da masu aikata laifuka, ta hanyar amfani da bayananta.
An yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda suke cudanya da juna tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu na aikata laifuka ba tare da an gane su ba, lamarin da ya sa ake bukatar gaggawar samar da matakan da suka dace don bin diddigin mutanen da kuma kama su.