A yau ne, Sanata Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattijan Nageriya Malam Uba Sani ya ce, Majalisar Nageriya ta amince da kudurin gyaran dokar hana yaduwar bindigogi a cikin al’uma na Cap. F28.
Uba Sani ya bayyana Murnar shi ne a cikin wani rubutu daya wallafa a shafinsa na facebook Yana mai cewa, ” Sashin dokar Najeriya, na gyararriyar dokar shekarar 2004 ya amince da wannan kudurin a shekarar 2021 mai lakabi da (SB 549). Inji Sanatan.
“Shugaban majalisar dattijai, mai girma Sanata Ahmad Lawan ya nuna matukar jindadinshi game da wannan kokari da na yu, inda ya bayyana cewa wannan kudurin doka ne daya dace, da kuma ya cancanta shugaban kasa ya ba shi cikakken goyon baya”
Wannan Kuduri na neman yin kwaskwarima ga Dokar Makamai a kundin tsarin dokar kasar nan na Cap. F28, na shekarar 2004.
1. Wannan kudirin dokar zai Kara karfafa tara ga laifuka ƙarƙashin dokar tsarin mulki na yanzu, wanda ba shi da wani cikakken ƙarfi a baya.
KARANTA WANNAN : Sanata Kabiru Marafa ya yi Jurwaye Mai kama da wanka
2. Kafa wani cikakken tsari dazai hada karfi da karfe, da kuma lalata dukkanin makaman da ya shiga cikin al’uma ba bisa ka’ida ba, daga Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro domin hana bindigogi sake shiga cikin al’ummominmu..
3. Ci gaba da fitar da dabarun yin doka yadda ya kamata, tare da daukar kwararan matakai, don magance dalilan da ke taimakawa yaduwar bindigogi, ba bisa ka’ida ba, tare da toshe duk wata kofa da ake kokarin samar da muggan bindigogi a cikin kasar.
Sanatan ya Kara da cewa kididdiga kan yaduwar haramtattun makamai, da haramtattun kayayyaki a Afirka ta Yamma, musamman a Najeriya ya ja hankali na, da kuma yanke shawarar daukar nauyin wannan Kuduri. daga kididdigar da aka samu daga Cibiyar Kula da Zaman Lafiya da kwance damarar makamai, da adana kayayyaki ta Abuja
Ya ciga ba da cewa, an ba da rahoton cewa, yaduwar kananan makamai ba bisa ka’ida ba a Najeriya ya kai matuka.
” Kuma sama da Miliyan 500 na irin wadannan makamai ne ke yawo a Yankin Yammacin Afirka, yayin da sama da Miliyan 350, ke wakiltar kashi 70% na irin waɗannan makamai suna cikin gida Najeriya” Inji shi.
Ya cigaba da cewa, barin afkuwar irin wadannan acikin jama’a abun takaici ne Matuka, sabida haka ya sa a ke son samar da wannan dokar, domin samar da tsaura-ran hukunce-hukunce da za su zama matakan dakile wannan lamari. a kokarin da ake yi na dakile yaduwar muggan makamai da dukkan laifukan da ke tattare da hakan a cikin al’uma.
Kudurin ya bi ta hanyar halartar da aka samu da kuma sakamakon sauraron Jama’a. Masu ruwa da tsaki baki daya sun goyi bayan amincewa da kudurin dokar tare da kwaskwarima, wadanda suka bayyana a cikin daftarin kudirin da aka gabatar wa majalisar dattijai don amincewa da shi.
Bayan cikakken nazarin rahotonni kwamitocin majalisar dattijai, Wanda suka hada da kwamiti kan harkokin shari’a, yancin dan Adam, da kuma lamuran shari’a, majalisar dattawan ta amince da wadannan gyare-gyare:
1. Dokar ta kunshi cewa, tarar da ake a Sanya wa masu laifi, a dokar da ta gabata ba ta yi dai-dai da nauyin laifin ba, sabida haka Karin da akayi na tarar a cikin kudurin dokar, zai zama abin hanawa da kuma karfafa kokarin da ake yi, a halin yanzu na shawo kan Batun Haram ta muggan makamai, dake kwararowa cikin kasar nan, tare da Samun mallakarsu ga mutane;
2. Cewa yin amfani da bindigogin da aka kwace, da wadanda aka kama, dokar zata yi amfani ta hanyar soja ko kungiyoyin sa kai, da su ka da ce, da kyawawan halaye da ake iya samu a wasu yankuna kasashen waje kamar Amurka, Indiya, Ostiraliya, da sauransu; kuma
3. Cewa kwaskwarimar da Kwamitin ya gabatar, wanda ke neman shigar da wasu hukumomin karfafa doka a cikin sashe na 38 na sabuwar dokar, wani ci gaba ne, da maraba sabida, ba jami’an Sojojin Tarayya da na ‘Yan Sandan Najeriya ka dai ba ne, suke da izinin ɗaukar bindigogi da alburusai yayin aiwatar da ayyukansu na doka.
A Karshe Sanatan ya yi godiya ga majalisar, inda yake cewa ina matukar godiya ga Shugaban Majalisar Dattawa, Kwamitin Kula da Shari’a, ‘Yancin Dan Adam, da kuma na Harkokin Shari’a, da dukkan Sanatoci masu daraja ga me da wannan matakin. Wannan muhimmiyar gudummawa ce, mai mahimmanci ga ƙoƙarin da aka tsara, don ƙasƙantar da masu aikata laifuka a Nijeriya, da kuma dawo da zaman lafiya ga al’ummomin da ke cikin rikicin..
Da ake fira dashi a Gidan Radio na Freedom Kaduna, Idan baku manta ba a wannan makon da muke ciki ne, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, “Kawo yanzu Tsawon Zaman sa a majalisar dattijan Nageriya ya gabatar da kudrirori goma Sha Tara 19, tare da kawo aiki sama Dana Bilyan biyar Wanda ba’a taba Samun wani Sanata da yayi hakan, ba a Tarihin Jihar kaduna” Inji Sanatan.
Comments 3