A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka ruwaito wata malamar Sakandare a jihar Ogun, Misis Oluwatosin Aina, ta suma a harabar makarantar da take aikin koyarwa,kuma daga baya aka bayyana mutuwarta.
Misis Aina, malama ce a babbar makarantar Olokinne, Ojowo, Ijebu Igbo a karamar hukumar Ijebu ta Arewa dake jahar Ogun.
Misis Aina wacce aka ruwaito ta tuka kanta zuwa makaranta ranar Alhamis, an ce ta fara jin zazzabi bayan ta isa makarantar.
A wani labarin kumaMataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gana da Wasu Gwmnoni a Ogun, Ya Bukaci Hadin Kan Najeriya
Jami’ar da ke karantar da ilimin addinin Kirista a matakin albashi na 14, an ce ta samu izini daga shugaban makarantar domin ta je ya kula da lafiyarta amma tabfadu ta suma a kusa da motarta, sannan aka garzaya da ita zuwa sashin asibitin koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOUTH). Ijebu Igbo inda aka tabbatar da mutuwar ta.
Rahotanni sun ce lamarin ya jefa makarantar gaba daya cikin makoki ganin irin sadaukarwa da soyayyar marigayin ga dalibai da abokan aikinta.
An ce Misis Aina ta wuce shekara 50 kuma ta auri wata shugabar makaranta mai ritaya a yankin Ijebu Igbo.
A wani labarin kumaHar Yanzu Akerodolu Ne Gwamnan Ondo-Shugaba Tinubu
A daren Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki bijimin ta hanyar shiga cikin rikicin shugabanci da ke barazana ga zaman lafiyar gwamnatin jihar Ondo inda ya bayyana cewa Gwamna Rotimi Akeredolu ya ci gaba da zama shugaban zartarwa na jihar.
Shugaban ya shiga tsakani ne a yunkurinsa na maido da kwanciyar hankali a siyasance a rikicin da aka kwashe watanni ana yi tsakanin bangarorin da ke biyayya ga Gwamnan Zartarwa, Rotimi Akeredolu, da Mataimakin Gwamna Lucky Aiyedatiwa.