Ministoci uku da suka janye daga halartar zabukan fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulki a ranar Laraba sun halarci taron majalisar zartarwa ta tarayya.
Mambobin majalisar ministocin da abin ya shafa da suka halarci taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta sun hada da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) da ministan shari’a, Abubakar Malami; Ministar harkokin mata, Pauline Tallen; da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva.
Yayin da Malami ya fara shiga taron majalisar ministocin a yau, Tallen da Sylva sun shiga daga bisani.
AGF ya nuna sha’awar zama Gwamnan Jihar Kebbi; Ministar harkokin mata ta dauki fom din tsayawa takarar kujerar Sanata a jihar Filato, yayin da takwararta ta, na ma’aikatar albarkatun man fetur ya bi irin wannan hanya domin samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban ya yi bankwana da ‘yan majalisar zartarwa ta tarayya da suka bar aiki a wani takaitaccen biki da aka gudanar a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Sai dai wasu daga cikinsu da suka hada da Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige, Malami, Sylva, da Tallen sun janye daga takarar bayan sun halarci taron.
A halin da ake ciki kuma, kafin a fara taron na FEC, an yi shiru na minti daya don karrama tsohon ministan sadarwa na gwamnatin Janar Ibrahim Babangida, Olawole Adeniji Ige, wanda ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya halartaci taron; Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (HOCSF), Dr. Folasade Yemi-Esan, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (mai ritaya).
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministocin Watsa Labarai da farfado da Al’adu, Lai Mohammed, Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello, Minsitan kula da sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, minsitan Sadarwa da Tattalin Arziki Isa Pantami, Minsitan Muhalli, Mohammed Abdullahi, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare na Kasa. , Zainab Ahmed, Minista Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, da Minsitan kula Harkokin da harkokin kasashen Waje, Geoffrey Onyeama
Sauran sun hada da Karamin Ministan Lafiya, Olorunimbe Mamora, Minsitan Noma, Mustapha Shehuri da kuma kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clem Agba.
Comments 1