A kokari da takeyi na yaki da zazzabin Cutar cizon Sauro, ƙasar Malawi ta fara yi wa yara allurar rigakafi cutar a matsayin wani bangare na yaki da zazzabin cutar malariya a duniya. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Kamfanin haɗa magunguna na GSK da ya shafe sama na tsawon shekaru 30 yana aiki, kafin ya samar da Alurar rigakafin samfurin RTSS .
KARANTA WANNAN LABARIN : 2023: Ɗan Tsohon Gwamnan Ya Lashe Sabon Zaben Fidda Gwanin APC da Aka Canza
Rahotanni sun nuna cewa gwajin farko na rigakafin ya nuna sama da kashi 30 cikin ɗari na yara yan watanni biyar zuwa 17 da akawa rigafin za su samu kariya daga cutar.
Kasar Malawi ta yi ammanna cewa har yanzu za ta bada muhimmiyar gudummawa wurin yaki da cutar da ta kashe jarirai kimanin 2,500 a kasar, shekaru biyu da suka gabata .
A nasa ɓangaren Shugaban shirin kawarda cutar malariya na ƙasar ta Malawi , Dakta Michael Kayange ya faɗawa wani shirin kafar yada labarai ta BBC mai suna “Focus on Africa” cewa, suna da masaniya kan rashin ingancinsa wajen dakile cutar zazzabin cizon sauro amma babu wani mataki da za su ɗauka kai tsaye.
Tsawon shekaru da dama Cutar malariya dai ta kasance daya daga cikin manyan kalubale da al’umma ke fuskanta inda take sanadiyar rasa rayukan mutane da dama galibi cutar tana kashe jarirai da ƙananan yara.
Cutar dai tana yaduwa ne ta hanyar cizon mace sauro.
Kana Bayanai sun nuna cewa, cutar na shafar nahiyar Afirka sosai.
A shekarar 2020 an ƙiyasta cewa , kashi 95 na mutane a nahiyar Africa sun kamu da cutar sannan kashi 96 cikin dari na waɗanda suka kamu da cutar ke mutuwa.
Bayanai daga hukumar lafiya ta duniya, (WHO) tace yara yan kasa da shekaru biyar ne ke da kashi 80 na yawan mace-macen da ake samu daga zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka.
Sai dai Dr Kayange ya ce, sabon shirin rigakafin cutar za a tabbatar da cewa duk yara yan kasa da shekaru biyar, har da waɗanda ke zaune a yankunan karkara a kasar sun karɓi rigakafin.
Kazalika kashi na farko dai zai gudana a yankuna 11 daga cikin 28 na kasar ta Malawi, inda ake sa ran yiwa yara 330,000 allurar rigakafi a kashi farko kadai.
A wani labarin kuma, Za Mu Tabbatar An Gudanar Da Zaben 2023 Lami-Lafiya— Lucky Irabor
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Janar Lucky Irabor, ya ce rundunar sojin Najeriya na aiki tukuru domin ganin an gudanar da zaben shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali a fadin kasar nan.
Irabor ya bayyana haka ne a ranar Talata a hedkwatar rundunar tsaro ta Operation Safe Haven, da ke aiki da jami’an tsaro da dama da ke wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, yayin da yake kaddamar da wasu ayyuka da kwamandan rundunar Janar Ibrahim Ali ya aiwatar.