An gano cutar zazzabin cizon sauro na a matsayin babbar mai cuta mai kisan ‘yan Najeriya, a yankin kudu da hamadar Sahara na Afirka tsawon shekaru.
Kungiyar yaki da kwari ta Najeriya, PECAN, reshen Abuja, ta ce cutar zazzabin cizon sauro ta kashe ‘yan Najeriya fiye da Boko Haram, da ‘yan bindiga, da kuma duk wani yaki da aka kwashe shekaru ana yi.
Shugaban kungiyar PECAN reshen Abuja, Terungwa Abari ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yayin wani taron wayar da kan jama’a domin tunawa da ranar zazzabin cizon sauro ta duniya ta bana.
A cewar Abari: “Sauro ya kashe ‘yan Najeriya da mutane fiye da Boko Haram da duk wani yaki ya kashe, kuma yana illa fiye da cutar HIV da sauran cututtuka.
PDP Ta Caccaki Jam’iyyar APC Kan Kiran Da Ta Yi Na A Tsige Gwamnan Arewa
A cikin shekaru sama da 200,000 na bil’adama, mun sami karuwar al’umma kusan biliyan ɗari, kuma za ku yi mamakin sanin cewa sauro ya kashe kusan rabin mutane biliyan 52 tun farkon halittar ɗan adam.
“Alkaluma na karshe na WHO sun nuna cewa sauro ya kashe kusan mutane 600,000, kuma rabin wadanda suka fito daga Najeriya da wasu kasashe shida, kuma Najeriya ce ke dauke da mafiya yawa. Don haka, za ku iya gane girman matsalar da muke fuskanta idan ta zo ga batun matsalar sauro.
Da yake jawabi ga manema labarai, Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi, ya koka da cewa zazzabin cizon sauro na da tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.
Abdullahi wanda babban magatakardar hukumar kula da lafiyar muhalli ta Najeriya Yakubu Baba ya wakilta ya ce a shirye suke wajen turawa da kwararru da sabbin fasahohi don kawar da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya.
A cewarsa Kawar da cutar zazzabin cizon sauro a cewar shugaban kasar, zai rage wa tattalin arzikin kasar zirarewa da sama da Naira tiriliyan biyu.