Kasar Mali ta karbi jiragen yaki da kuma jirage masu saukar ungulu daga kasar Rasha a daidai lokacin da Moscow ke kara samun karbuwa a cikin kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Tun bayan katse hulda da Faransa, gwamnatin mulkin soji a Mali ta dogara ga sabuwar kawarta wato Rasha, wanda ta tura sojojin haya daga kungiyar Wagner a cewar majiyoyi da dama.
KU KARANTA: 2023 Zata Zama Mai Tsauri Ga Masu Fasa Gidan Yari – NCoS
Masu aiko da rahotanni sun ce wadannan sojojin ba su yi komai ba a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, da masu tsatsatsaurar ra’ayi akan addinin Islama, kuma da alama sun mayar da hankali ne wajen samun albarkatun ma’adinan Mali domin cin moriyar su.
Ana kuma zargin Rasha da shiga cikin wata kasa ta Afirka da ake kira Eswatini, ko da yake jakadan Moscow a kasar Alexander Surikov ya musanta rahotannin da ke cewa tana horar da jami’an tsaro a can.
A wani labari kuma, Buhari Ya Tarbi Sabon Mai Tsaronsa
A ranar Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabon kwamandan rundunonin tsaronsa Birgediya Janar AM Umar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Umar ya karbi ragamar Jagorancin rundunar ce daga hannun Birgediya Janar Mohammed Usman wanda aka yi masa sauyin wurin aiki makwanni biyu da suka gabata.