Jam’iyyar APC a jihar Edo ta yi tir da sauya shekar mambobinta zuwa jam’iyyar PDP.
Yan siyasar dai sun ce sun fice daga APC ne saboda zargin shirya makircin wa Sanatan Edo ta Arewa, Francis Alimikhena a zaben fidda gwani da aka yi a watan Mayun da ya gabata.
Tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole ne ya lashe tikitin takarar gundumar kuma zai fafata da Alimikhena, wanda a yanzu dan takarar PDP ne.
Wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Victor Osheobo ya fitar ta ce ficewar da aka ce, shugabannin Jam’iyar 64 a jihar sun yi, “Adadi ne na karya”.
Kakakin ya shaida wa jam’iyyar PDP cewa ta yi hattara da yaudarar kai da aka yi mata na bogi da wadanda ba su da tushe balle makama.
Osheobo ya kuma bayyana cewa babu daya daga cikin wadanda suka sauya sheka da zai iya samun rinjayen magoya baya daga yankunan su
Ya kuma bayyana tsofaffin Mambobin Jam’iyar na APC da suka sauya sheka domin marawa gwamna a matsayin maciya amana, .
“Biyu daga cikin wadanda suka sauya shekar, kamar Sabata Francis Alimikhena da Mista Lucky James, sun zama manya kusoshi ne a cikin jam’iyar mu”
Sanarwar ta bayyana James a matsayin dan kasuwan a fannin siyasa, “wanda kwadayinsa da rashin jin dadinsa shine ya fi baiwa mahimmanci”.
Osheobo ya kira jam’iyyar PDP ta Edo a matsayin jam’iyyar siyasa da ta nutse wacce ta ke yi rayuwarta kawai akan cin amana da karya da zamba da kuma farfaganda.