A ci gaba da buga gasar Firimiyar Ingila, a daren jiya Talata, kungiyar Manchester United ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Southampton da ci 9 da nema.
Wasan wanda aka buga shi a tsawon minti casa’in, an fara zura kwallon farko ne a minti na 18 wanda Aaron Wanna-Bissaka ya zura.
Sauran wadanda suka zura kwallon sun hada da Anthony Martial, inda ya ci kwallo biyu, sai Cavani, Rashford, McTominay, Fernandes, James, inda suka zura kwallo daya-daya.
Shi kuma Bednarek ya ci kansu da kan shi.