A cigaba da zaɓen fitar da gwani da Jam’iyu ke yi a fadin kasar nan domin shirin tunkarar kakar zaben 2023, a jiya Laraba Jam’iyar PDP Mai adawa a jihar Kebbi ta fitar gwaninta da zai mata takarar neman gwamnan jihar.
Zaɓen wanda aka fafata tsakanin yan takarar guda biyar ya samu hallatar wakili hukumar zaɓe, masu sa ido da yan jaridu da dama.
Tuni dai aka ayyana Janar Aminu Bande mai ritaya a matsayin wanda yayi Nasara a Zaben.
Da yake jawabi bayan kammala girga kuri’un da aka kada shugaban zaɓen Mr Peter ya yabama wakilai masu zaben yan takara wato Delegate, jamiyan tsaro yan jarida hukumar INEC da dai sauransu kan irin gudunmawar da suka bayar wurin gudanar da zaben lami lagiya.
Shugaban ya bayyana adadin wakilai masu zaben da aka tantance guda 690, yayin da yawan kuri’un da aka kada suka kai 685, inda daga cikinsu aka samu biyu da suka lalace.
Shugaban zaben ya sanarda sakamakon kuri’un da kowa wane dan takara ya samu kamar haka;
Janar Aminu Bande mai ritaya ya samu kuri’u 471, Yayinda
Alhaji Ibrahim Abdullahi da yazo na biyu da kuriu _126, Sai Bala Buhari da yasamu Kuri’u _43, sai Alhaji Garba Haruna Argungu ya samu kuri’u 22, yayin da stohon dan takara gwamnan a jamiyar ta PDP a shekarar 2003 Sama’ila Sambawa ya tashi da kuriu _21, inda aka samu kuri’u 2 da suka lalace.
Da yake jawabi jim kadan bayan ayyanashi a matsayin wanda yayi Nasar lashe zaben fitar da gwanin, Janar Aminu Bande mai ritaya , ya godewa Allah subhanahu wata’ala akan nasarar da ya samu, haka kuma ya bama kwamitin da suka shirya zaben akan yadda aka gudanar da zaben bisa gaskiya da adalci.
Kana Aminu Bande ya nuna godiyarsa ga dukkanin abokan takarar sa bisa Yadda sukabi dokokin da aka tsara wurin gudanar da zaɓen.
Yanemi dukkanin waɗanda sukayi takarar tare da su zo su haɗa hannu domin ta fiya tare.
A halin yanzu dai manya da kananan jam’i u daban daban na ci-gaba da shirin tunkarar kakar zaben mai zuwa.
A yau Alhamis ne ake sa ran jam’iyar APC mai mulki zata Fara fitar da nata gwanayen da za suyi mata takarar mukamai a kakar zaben da ke tafe.