Manyan ƴan siyasa na shirye-shirye tsige Shugaban Majalisa akan zargin zama ɗan Amshin Shata ga Gwamnati
Manyan ‘yan siyasa da ke adawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na shirin tsige shi idan Majalisar Dattawa ta koma aiki bayan hutun da suka tafi a ƙarshen wannan watan.
Rahotanni sun nuna cewa Sanatocin sun ji haushin yadda tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya zama Ɗan Amshin Shata ga Shugaba Tinubu maimakon biyan buƙatun ‘yan Majalisar da ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Sun yi zargin cewa kusancin da ke tsakanin Akpabio da Shugaban ƙasar ya sa ba ya mai da hankali ga abokan aikin sa da kuma yin aiki tukuru domin cimma burin ‘yan Najeriya duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wasu daga cikin Sanatocin da suka fusata da Shugaban Majalissar akwai wasu tsaffin Gwamnonin Arewa maso Yamma guda biyu inda suke son yin amfani sakon kwanan nan da Akpabio ya saki, inda yace “an aika da addu’o’i a akwatunan wasikunsu domin yin bukukuwan Hutu” sun ce domin hukunta shi.
KARANTA NAN:Yadda Kogunan Ogun Suka Hallaka Sama Da Mutane 50
Wata majiya mai tushe a Majalisar da ta san shirin da ake ƙullawa ta ce tuni kungiyar ta ƙin goyon bayan Akpabio ta gudanar da tarurruka da dama a Saudiyya da Ilorin domin kammala shirye-shiryen tsige shi idan Majalisar Dattawa ta dawo.
Babban majiyar NASS ta ce “Daga cikin laifukan da Sanata Akpabio ya yi akwai zargin da ake yi masa na tsananta alaka da Shugaba Bola Tinubu.
Har ila yau, suɓul da bakan da Shugaban Majalisar Dattawa ya yi a ranar da za a dage zaman zuwa hutu, sun ce shi za su riƙe a matsayin makamin da za su yaƙi Akpabio.
An tattaro cewa, duk da cewa Shugaban Majalisar Dattawan ya fayyace abin da yake nufi Ma’ana addu’a, tare da janye kalamansa, bai yi wa da yawa daga cikin abokan aikinsa daɗi ba, wadanda suka bayyana damuwarsu a bainar jama’a.
Dukkan waɗannan abubuwan shirye-shirye ne na tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 inda ake sa ran kafa wata sabuwar Jam’iyya mai suna “hybrid party” inji majiyar na kusa da ‘yan Majalisar da jami’an tsaro.
Wasu Sanatoci na shirin tsige Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio “ Zan iya faɗa muku da kwarin guiwar cewa akwai Sanatoci hudu da ke Jagorantar shirin kuma biyu daga cikin su tsofaffin Gwamnoni ne daga shiyyar Arewa Maso Yammacin kasar nan”, Majiyar ta ƙara.
Domin tabbatar da shirin nasu, sun gana a ƙasar Saudiyya kwanan baya da kuma a Ilorin babban birnin Jihar Kwara da manufa ɗaya na tsige Shugaban Majalisar dattawan.” Majiyar ta bayyana.
Sun yi niyyar maimaituwar wani tsunami da ya afkawa Jam’iyyar PDP ga APC ta yanzu, irin yadda PDP mai mulki a lokacin a shekarar 2014 jiga-jigan Jam’iyyar da dama suka koma suka kafa Jam’iyyar APC a yau.