Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce wasu manyan jami’an ‘yan sanda 130 da ke jiran ladabtarwa (PDM) sun gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na rundunar a hedikwatar rundunar (FHQ) da ke Abuja.
A gobe ne za a kawo karshen binciken da aka fara tun ranar 28 ga watan Yuni.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/kwamitin-shugaban-kasa-kan-shirin-kwallon-kafa-ya-kammala-aikin-sa-galadima/
Jami’in hulda da jama’a na rundunar (FPRO) Olumuyiwa Adejobi, yace CSP na ‘yan sanda ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya a Abuja.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Jimillar manyan jami’an ‘yan sanda 130 daga ko’ina a fadin kasar nan masu jiran gado (Pending Disciplinary Matters) za su bayyana a gaban kwamitin a cikin wannan lokaci.
“Jami’an sun hada da kwamishinonin ‘yan sanda biyu, mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda uku, manyan Superintendents na ‘yan sanda 11, Superintendents ‘yan sanda 19, mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda 18, da mataimakan Sufiritanda 77.
“Bayan an kammala shari’a da kuma sauraron shaidu, za a sanar da shawarwari kan kowane lamari ga Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) don tantancewa.
“Shugaban rundunar ya bayyana kwarin gwiwa ga DIGs da ke kula da kwamitin ladabtarwa na rundunar domin tabbatar da gudanar da shari’a a duk wani abu da ke gabansu.
Hakazalika, IGP din ya tabbatar da cewa rundunar ta himmatu wajen tsaftace gidanta domin samun ƙwararrun tsarin ‘yan sanda da ya mai da hankali ga ‘yan ƙasa.”