By Abbas Yakubu Yaura
A halin yanzu dai masu ababen hawa dake kan hanyar Onitsha zuwa Owerri na kokawa kan yadda hanyar ta tabarbare.
Hanyar dai wacce ta hade gadar Neja zuwa Ihiala, Orlu, Owerri, Aba da kuma jihohin Kudu maso Kudancin kasar.
Wakilinmu ya tattaro cewa, rashin kyawun hanyar yana haifar da cikas sannan kuma yana haifar da karuwar lokacin tafiye-tafiye da kuma kudin sufuri zuwa kashi 100 cikin 100.
Shugaban kungiyar ma’aikatan zirga-zirgar ababen hawa ta Najeriya reshen jihar, Mista Samson Ede, a ranar Larabar data gabata ya yi nadamar cewa gwamnati, a dukkan matakai sun yi watsi da hanyar, wanda a cewarsa, ita ce “hanyar kofar” data hada sauran jihohin Kudu maso gabashin kasar.
Ede yace, “Wannan titin hanya ce mai matukar muhimmanci ta kasuwanci wadda sama da kashi 70 cikin 100 na matafiya dake zuwa Kudu maso Gabas suna amfani da ita a kullum. Mummunan yanayin lalacewar ta yana bamu damuwa sosai, musamman yayin da muka shiga kololuwar lokacin bukukuwan karshen shekara dana sabuwar shekara.
“Yana kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a ciki da wajen Anambra.Ko da yaushe zirga-zirgar ababen hawa suna cikin rudani a dukkan hanyoyin biyu.Idan gwamnati zata iya samar da wasu matakan kwantar da hankali, za ta yi nisa don rage radadin wahala musamman a wannan lokacin bukukuwan da mutanenmu zasu dawo gida.”
Wani dan kasuwa, Mista Raphael Obat, a nasa bangaren, yace yanayin hanyar ya tilastawa mutane barin motocinsu.
Sannan ya ce, “Abin takaici ne yadda aka dade ana watsi da hanyar kasuwanci irin wannan, duba da cewar Kudaden jigilar kayayyaki na kara karuwa a kullum, wanda hakan ke janyo tsadar farashin kayayyaki da ayyuka a kasuwa”.
Da aka tuntubi kwamishinan ayyuka na jihar, Marcel Ifejiofor, yace hanyar ta gwamnatin tarayya ce bata gwamnatin jiha ba.
Sai dai kuma duk kokarin tuntubar mai kula da ayyuka na tarayya a jihar don jin ta bakinsa yaci tura har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.