Babban Daraktan, kungiyar Esan Youth for Good Governance and Social Justice, Benson Odia, a ranar Litinin din nan, ya ce masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da fasinjoji a tashar jirgin Tom Ikimi da ke Igueben, Jihar Edo a ranar Asabar din da ta gabata, sun tuntubi wasu iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.
A cewarsa sun bukaci Naira miliyan 20 ga kowane wanda abin ya shafa a matsayin kudin Fansa.
KU KARANTA: Al-Nassr Ta Fara Kai Cafka Kan Dan Wasa Sergio Busquets
Odia ya ce bukatar ta nuna ƙarara irin hankalin su, inda ya yi kira ga hukumomi da su kara zage damtse wajen kubutar da mutane 31 da aka sace wadanda har yanzu suke hannun wadanda suka sace.
Ya kuma ce Ministan Sufuri da Shugaban Kamfanin Jiragen Ruwa na Najeriya sun kasance a Igueben don tantance halin da kansu.
Odia ya ce hukumomi sun yi alkawarin yin amfani da jirgi mai saukar ungulu a ranar Talata a kokarin gano inda aka ajiye wadanda abin ya shafa a cikin daji.
Ya ce, “Zan iya gaya muku cewa masu garkuwa da mutane sun bukaci Naira miliyan 20, jimlar Naira miliyan 620.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce zai tabbatar da gaskiyar batun zuwa nan gaba.
A wani labarin kuma: Tsohon Dan Wasan Man United Ighalo Ya Sanar Da Gwaninsa A Fadin Duniya
Tsohon dan wasan Manchester United, Odion Ighalo, ya zabi dan wasan Real Madrid, Karim Benzema, a matsayin wanda ya fi kowanne dan wasan gaba a duniya.
Ighalo, wanda a halin yanzu yake taka leda a kulob din Al Hilal na Saudi Arabiya, ya yi imanin cewa Benzema ya yi fice a shekaru biyun da suka gabata.