Wasu ‘yan bindiga sun kashe babban dan dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Dass, Bala Ali, kwanaki kadan bayan sun yi garkuwa da shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Burra, Ado Wakili, ya bayyana hakan a jiya a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Danlami Ahmed Kawule ya jagoranta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan ta’addan IPOB Sun Kashe Sojoji 5 Da Farar Hula A Anambra
Da yake tabbatar da hakan, Abubakar Dambam mai wakiltar mazabar Dambam/Zagaya/Jalam, ya bayyana cewa tuni aka gudanar da Sallar jana’izar marigayin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro da takaici.
Mataimakin shugaban majalisar ya bada umarnin a gudanar da addu’a ta musamman ga marigayin wanda Bello Muazu Shira mai wakiltar mazabar Shira ya jagoranta.
Ya kuma bayyana cewa majalisar za ta kai ziyarar ta’aziyya ga yan uwa da iyalansa a garin Dass.
A WANI LABARIN KUMA: Kotu Ta Tasa Keyar Wani Mutum Gidan Yari, Bisa Lalata Da Wata Yarinya
Wata Kotun Majistare da ke Osogbo a Jihar Osun ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 37, Abiodun Babatunde, a gidan yari na Ilesa bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara hudu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ana tuhumar Babatunde da laifuka guda hudu da suka shafi jima’i ba bisa ka’ida ba, cin zarafi da kuma barazana ga rayuwa.