rundunar yan sandar Jihar Kaduna dake aikin karkashin shirin nan na Operation Puff Adder ta kubutar da mutane takwas daga hannun masu garkuwa da mutane a karmar hukumar Giwa ta jihar.
Mutanen an sace su ne a ranar 29 ga watan Jiya a hanyar Zaria zuwa Kaduna yyain da suke shirin ketare jiha zuwa Jihar Delta a wata mota kirar Bas.
Cikin wata sanarwa da Kakain rundunar yan sandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya fita ya ce rundunar Operation Puff Adder ta fito sintiri ne a rnar Litinin inda ta yi kicibis da wasu masu garkuwa da mutane a kauyen Galadimawa da Kidandan dukkanin su a karmar hukumar ata giwa.
A cewar shi, rundunar ta samu bindiga kira AK47 da yan bindiga suka arce suka bari tare da ceto mutane takwas ciki har da mace wanda aka ceto din ba tare da ko kwarzzani ba.
Kakakin ya ce yan fashin dajin sun hango rundunar ne inda suka fara rantawa a na kare suna barin mutanen da suka sace.