Masu zanga-zangar karkashin jagorancin kungiyoyin kwadago sun balla kofar majalisar tarayya da ke Abuja
Masu zanga-zangar wadanda shugaban kungiyar ‘yan kwadago ta Najeriya, NLC, Joe Ajaero, da Festus Osifo na kungiyar ‘yan kasuwa, TUC ne ke jagorantar zanga-zangar, sun bukaci jami’an tsaro da ke a harabar majalisar da su bude kofa domin ma’aikata su tattauna da ‘yan majalisar
Amma jami’an tsaron sun ki amincewa. A fusace masu zanga-zangar suka ruguza kofofin suka mamaye harabar majalisar
Wasu jami’ai sun yi musu jawabi daga cikin masu zanga zangar inda suka bukaci a kawo karshen kuncin rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da yan kasar ke fama dashi
Babban mai tsawatrwa na majalisar dattawa, Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu), ya bukaci shugabannin kwadago da masu zanga-zangar da su janye zanga-zangar da ake yi a fadin kasar, su baiwa majalisar dattijai mako guda ta magance bukatun da aka kawo mata
KARANTA NANJuyin Mulkin Nijar-Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS Na Taro A Abuja
A halin da ake ciki kuma, a Legas, kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin jihar ta ba da tallafin Naira 30,000 don rage wahalhalun da ake fama dasu ta hanyar cire tallafin man fetur
Shugaban kungiyar NLC ta Legas, Funmi Sessi ce ta yi wannan bukata lokacin da mataimakin gwamnan jihar, Kadri Hamzat, ya yi jawabi ga masu zanga-zangar
Sessi ta ce: “Muna bukatar tallafi Mafi ƙarancin albashinmu ba zai iya ɗaukar nauyinmu ba
Mutane da yawa suna mutuwa, kuma suna jin yunwa. Mun san gwamnatin jihar tana kokari, amma har yanzu suna bukatar kara yin hakan
Muna bukatar tallafin Naira 30,000 kowanne ga ma’aikata, na tsawon watanni shida masu zuwa
A WANI LABARIN KUMABai kamata Gbajabiamila da Alake su tattauna da NLC ba – Shehu Sani ya bayyana kurakuran Tinubu
Mun san gwamnati ta rage farashin kudin BRT, amma muna son mu iya sanya abinci a teburinmu. Wasun mu suna da motoci, muna bukatar mu sayi mai