Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi ya fice daga jam’iyyar APC inda ya arce zuwa jam’iyyar PDP.
Ajayi ya fice daga APC din ne a mazabarsa dake Ward 2 a Apoi, dake karamar hukumar Ese Odo a jihar.
Sai dai rahotanni sun ce ya zuwa ranar Litinin ake sa ran zai koma PDP a hukumance a Sakatariyarsu dake Akure.
Bayanai na nuni da cewa alakar dake tsakanin mataimakin gwamnan Ajayi da gwamna Oluwarotimi Akeredolu ta yi tsami a cikin watannin nan. Barinsa APC ya kawo karshen rade-radin ficewarsa a jam’iyyar.