Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Dan’Iya, ya musanta rade-radin ficewar sa daga jam’iyyar PDP, Punch ta rawaito.
Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abubakar, yayin da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho ya ce maigidan nasa ya yi watsi da rade-radin ficewar sa daga jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hotuna: Atiku Ya Kaddamar Da Makarantar Koyan Harshen Larabci a Kano
Sai dai Aminu ya tabbatar da cewa mataimakin gwamnan ya ci gaba da kasancewa dan takarar jam’iyyar PDP a jihar da kuma dan takarar sanata a jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Ya yi kira ga magoya bayan sa musamman ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar da su yi watsi da wasikar da ke yawo a kafafen yada labarai wanda ya bayyana a matsayin tunanin abokan hamayyarsa.
“Mataimakin gwamnan ya kira ni a waya yanzu ya sanar da ni cewa bai bar jam’iyyar a ko’ina ba, ya ce ya ci gaba da zama dan jam’iyyar PDP a jihar,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Tsohon PRO Na ‘Yan Sanda, Mba Ya Shiga Ofis Don Kama Aiki a Matsayin CP Na Jihar Ogun
Tsohon kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Frank Mba, a ranar Alhamis zai fara aiki a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mba dai zai karbi mukamin ne daga hannun CP Lanre Bankole, wanda aka tura hedikwatar rundunar dake Abuja.