By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Legas ta farko, Misis Adetoun Adediran, ta rasu.
Adediran, wacce ta kasance kafin rasuwar ta itace tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC, reshen jihar Legas, ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Kakakin jam’iyyar APC na Legas, Mista Seye Oladejo, ya tabbatar da haka a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.
Sannan ya ce, “ kafin rasuwar ta Tsohuwar shugabar mata ce a Legas ta tsakiya, ’yar siyasa ce wacce ta kasance kwakkwararriya kuma jajirtacciyar wajen ja-gorancin al’ummarta, sannan ta bada gudunmawa sosai wajen ci gaban jam’iyyar da ci gaban jihar Legas, Za a yi kewar ta sosai.”