Sanatan Borno ta Kudu kuma dan majalisar dattawa, Ali Ndume, ya ce shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin da ya dace ta cire tallafin man fetur.
Ndume ya ce gwamnatin Najeriya ta samu makudan kudade tun bayan da Tinubu ya bayyana cire tallafin.
Ya yi magana ne yayin da yake hira a wani shirin gidan talabijin na Channels, Siyasa A Yau ranar Juma’a.
A cewar Ndume dukkan ‘yan Najeriya kuma sun yarda cewa wasu daga cikin matsananciyar matsaya da ake bukata a dauka muddin ana bukatar ciyar da kasa gaba,akwai maganar cire tallafin man fetur.
Tinubu dai ya bayyana cire tallafin man fetur ne a lokacin kaddamar da shi a Abuja ranar 29 ga watan Mayu.
Gwamnatin tarayya ta yi asarar kusan N1.45tn daga kudaden da ta samu daga cire tallafin a tsakanin watan Yuni da Satumba.
Wannan ya fito ne a cikin takaddun rabon FAAC a shafin yanar gizon kungiyar gwamnonin Najeriya da Ofishin Kididdiga na kasa.
A wani labarin kumaYar Shekara 18 Za Ta Wakilci Nijeriya A Wata Gasar Kyau Ta Duniya
Gift Manayi, wata fitacciyar matashiya ‘yar shekara 18 da ke karatun digiri na farko a fannin Shari’a, kwanan nan ta samu kambu mai daraja a gasar Face of Beauty Beauty na Najeriya da aka gudanar a Legas.
Bayan nasarar da ta samu, Gift na shirin wakiltar Najeriya a gasar Miss Heritage International 2024 da za a yi a birnin Bangkok na kasar Thailand.
Kyawun kyan gani, hankali, da kuma jan hankalin Manayi sun burge alkalan, inda suka kai ta ga nasara a Face of Nigeria Beauty Preant. Nasarar da ta samu ya bude mata hanyoyin zama jakadiyar kyawa da al’adun Najeriya a matakin kasa da kasa.