- Yanzu haka dai an kama wata mata waliyar bogi ‘yar kasar Guinea, mai suna Fanta Sangaré, bayan da ta kama sallah a saman wani ruwa a lardin dake yammacin kasar
- Matar da ake zargin waliyar bogi ce ta ziyarci tekun kana kuma ta shimfida abin sallah a saman tafkin ruwan yayin da ta tsaya a kan shi don yin sallah
- Bincike ya nuna akwai karar da wani dan kasa ya shigar akan Fanta amma ‘yan sanda basu bayyana dalilin korafin ba
An kama wata mata waliyar bogi ‘yar kasar Guinea, mai suna Fanta Sangaré, bayan da ta tayar da hankali ta hanyar yin sallah a saman wani ruwa a lardin dake yammacin kasar, kamar yadda Correct NG ta rawaito.
An ce ta ziyarci tekun kana kuma ta shimfida abin sallah a saman tafkin ruwan yayin da ta tsaya a kan shi don yin sallah yayin da masu zuwa bakin tekun suka zuba ido cikin tsoro.
KARANTA WANNAN: Sabuwar Manufar Biza Tana Da Tsari Mafi Kyau Ga Najeriya — Jakadan Burtaniya
A cewar Africaguinee, ‘yan sanda na musamman na Taouyah sun kama Fanta a ranar Alhamis, 22 ga watan Yunin 2023.
Wani hoto da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna budurwar tana shawagi a kan saman ruwa yayin da take yin sallah wanda shine abinda ta sanya a gaba.
Sai dai jami’an ‘yan sandan da suka kama matar daga baya sun fayyace cewa laifin da ta aikata bai da alaka da yin sallar da take kan igiyar ruwa.
“Aikinta ba laifi ba ne. Me yasa aka kama ta akan hakan…?” An jiyo wani babban jami’in dan sanda yana fadar haka yayin da yake kallon abin mamaki.
Jami’in ya kara da cewa; “Yanzu haka tana can a (ofishin ‘yan sanda) tabbas, amma wannan na wani lamari ne na daban.
“Koke ne da wani dan kasa ya kawo zuwa ofishin na ‘yan sanda.”
Majiyar mu ta rahoto cewa bincike ya nuna akwai karar da wani ya shigar akan Fanta amma ‘yan sanda basu bayyana dalilin korafin ba.
A wani labarin kuma, NLC, TUC Sun Jinjinawa gwamnatin Zamfara kan biyan albashin wata 2 ga ma’aikatan jihar
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC reshen jihar Zamfara sun yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal kan biyan albashin watan Afrilu da Mayu.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban NLC na jihar, Kwamared Sani Haliru da takwaransa na TUC, Kwamared Sa’idu Mudi suka sanya wa hannu.