Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Aisha Matawalle, ta rabawa masu juna biyu har mutum dubu goma kayayyakin tarbar abin da za su Haifa. Rabon ya gudana ne a dukkanin kananan hukumomi 14 dake fadin jihar.
Ta rabawa kayayyakin ne a karkashin shirinta na “Mama Kit Care”. Matar gwamnan ta bayyana wannan aikin da ta yi ne a rabon karshe da ta yi a Gusau a ranar Alhamis, inda ya ce ta yi hakan ne domin taimakawa masu juna biyu da nufin bunkasa lafiyarsu musamman ga marasa karfi da suke karkara.
Mashawarciyarta ta musamman, Fatima Musa ce ta bayyana hakan, inda ta ce zuwa yanzu sun rabawa mata da adadinsu ya kai dubu goma a fadin jihar.