Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata mata mai suna Ramatu Yunusa mai dauke da ciki wata tara da aka sace a unguwar Damba da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ta haihu a sansanin ‘yan Bindiga.
A cewar mijinta, Mista Yunusa, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, NULGE, reshen jihar Zamfara, matar ta haihu da misalin karfe 3 na safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022 a sansanin ‘yan fashin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/neja-yan-taadda-sun-hallaka-yan-sanda-da-maaikata-sun-sace-yan-china-hudu-a-wurin-hakar-maadinai/
Ya ce bashi da damar da zai iya ganin matarsa da jaririyar.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ban sani ba ko jaririn da aka haifa namiji ne ko kuma yarinya amma abin da na sani shine matata ta haifi jaririn,” in ji shi.
A cewarsa, ‘yan fashin sun bukaci ko wanne irin abu a matsayin kudin fansa, inda suka jaddada cewa lamarin ya dame shi da iyalansa.
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa matar mai suna Ramatu Yunusa ma’aikaciyar jinya ce a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Gusau babban birnin jihar.
An sace ta ne da sanyin safiyar Talata, 28 ga watan Yuni, 2022, a gidanta da ke Damba a Gusau, babban birnin jihar.
Duk kokarin da ‘yan jarida suka yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura domin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu bai amsa kiran da aka yi masa ba.