Hajia Hajara Alkali, matar Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali, a ranar Talata ta tallafawa membobin kungiyar matan ‘yan sanda 50 a Edo da kayayyakin da za su taimaka musu wajen fara kanana da matsakaitan sana’o’i.
Hajia Hajara Alkali, wacce ita ce shugabar kungiyar matan Jami’an ‘yan sanda ta kasa (POWA), a jawabinta a Benin ta ce tallafin da ta bayar yana daga cikin manufofinta guda uku.
Ta lurantar da cewa yana da matukar amfani a ce kowacce mace ko uwa tana da hanyar rayuwa tare da taimakawa wajen tafiyar da iyali.
Ta kara da cewa; saboda wannan dalilin ne ta tallafawa membobin POWA wanda yana daya daga cikin manufofinta guda uku.
Shugabar kungiyar POWA din, ta nemi wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayayyakin a inda ya dace, inda ta ce za a ayyana kwamitin da zai rika bibiyar wadanda suka amfana da kayayyakin domin a ga wadanda ba za su yi amfani da shi ba za su sayar ne.
Ta kuma kara da cewa wadanda suka amfana da wadannan kayayyakin tallafin, wanda ya hada harda wadanda aka kashe wa mazaje da kuma mata wadanda suka yi ritaya yanzu za su iya dogaro da kansu.
Daga cikin kayayyakin da aka raba su akwai tandar suya ta masana’antu, iskar gas da silinda, injin dinki, injin niƙa, da kuma kuloli.
Tun da farko shugaban kungiyar ta POWA ya yaba da bikin yaye wasu membobin POWA a Edo daga Amena Academy.
A jawabinta a wajen taron, ta lurantar da cewa horon makwanni biyu da membobin kungiyar su 23 suka yi kan kananan kayan ciye -ciye da samar da abinci kungiyar ce nemo hakan, amma AFEDOSA Catering Services ce ta dauki nauyi.
Ta kara da cewa duk membobin da suka kammala karatun za a ba su jarin fara sana’ar.
Ta bukace su da su karfafa sauran membobin su yi rijista don samun horon tare da ba da ilimi da kwarewar da aka samu kan sauran membobin dake barikin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa matar IGP din a ranar Talata ta ba da kayan agaji da ya kai miliyoyin Nairori ga iyalan ‘yan sanda.
Kayan agajin sun hada da shinkafa, garri, mai, diapers, gishiri, sabulun wanka, sabulu, sabulun maganin kashe kwari da sauransu.