Wani dan kasuwa, Adeyinka Adeniyi, a ranar Talata ya shaidawa kotun Customary dake Ibadan cewa a raba aurensu da ya kwashe shekara 12 da matar bisa zarginta da neman kashe shi.
Adeyinka ya shaidawa kotun cewa matarsa Elizabeth ta neman kashe shi domin ta kwashi dukiyarsa. Adeniyi wanda yake zaune a Unguwar Ologuneru dake jihar Oyo, ya ce; matarsa Elizabeth shaidaniya ce.
“babban kuskuren da na yi a rayuwata shi ne auren Elizabeth. Ta sha zuba min guba da yunkurin murde min wuya”, ya tabbatar.
Ya ci gaba da cewa; “ya mai shari’a, ta yi hayar wanda zai kashe Ni bayan ta ga gubar da ta zuba min ya ki yin aiki”.
Har wala yau ya zargi Elizabeth da ta hada baki da wadansu ma’aikatansa a Otel domin a sace masa kudi.
Sai dai a martaninta, Elizabeth ta amince a raba auren amma ta karyata wadansu zarge-zargen da ya yi mata. Sannan ta nemi kotun da ta bata damar kula da ‘ya’yansu a wurinta.
“Ya mai shari’a, mijina Adeniyi ya take dukkanin ‘yancina. Ba ya barin ‘yan’uwana su ziyarce ni. Sannan ba ya biyan ma’aikatansa. Ya maishe da ‘ya’yana da ni kaina kamar Bayi. Muna yi masa aiki, yana kuma tilasta mana kwana a Otel dinsa da wurin aikinsa”. Ta tabbatar.
Alkali Ademola Odunade ya ce soyayyar dake tsakanin Adeniyi da Elizabeth ya gama lalacewa. Inda a karshe Alkalin ya raba auren.
Inda ya bai wa matar Elizabeth ci gaba da rikon karamin yaron, a yayin da mijin kuma mai suna Adeniyi zai yi rikon babban yaron.
Sannan Alkalin ya nemi mijin ya rika bai wa matar naira dubu biyar a duk wata domin kula da yaran dake hannunta.