Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta JAMB ta sake dage jarabawar gama gari da ake yi wa ‘yan takara a cibiyoyi 100 sakamakon kalubalen fasaha da suka fuskanta ranar Talata.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kori Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Da Wasu Mutane Bakwai
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ‘yan takara miliyan 1.6 daga sama da cibiyoyi 700 ne ake sa ran za su yi jarabawar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta kai ziyara a wasu daga cikin cibiyoyin yin jarabawar ta JAMB a jihar Kano, inda ta tarar da irin wannan matsala sai da ‘yan takarar suka shafe kusan sa’oi 2 suna jiran fasahar ta dai daita kafin daga bisani a cigaba da yin jarabawar.
Wakilinmu ya rawaito yadda na’urar daukar hoton yatsu taki nuna bayan wani dalibi yanaji yana gani akayi jarawar babu shi duk da kokarin da jami’an na JAMB suka yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Bayan sanarwar, ‘yan takarar da bisa dalilai na fasaha ba su iya yin jarrabawar ba, za su buga sabuwar sanarwar jarabawar da safiyar gobe Laraba, 26 ga watan Afrilu, 2023, domin sanin sabbin zaman da aka tsara.
JAMB ta ci gaba da cewa, “Abin lura ne cewa kusan cibiyoyi 100 daga cikin cibiyoyi 708 da suke gudanar da atisayen UTME na shekarar 2023 a fadin kasar nan, sun fuskanci kalubalen fasaha da suka hana wadanda aka basu damar yin jarrabawarsu.”
Ta cikin sanarwar, hukumar ta sake nanata kudurinta na tura kima na duniya daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya don sadar da ingancin kimantawa tare da yin nadama kan duk wata matsala da ‘yan takara da iyayensu suka samu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, jerin kalubalen da aka fuskanta sun biyo bayan wasu sabbin abubuwa ne da hukumar ta aike da su domin kare tsarkin jarabawar ta hanyar tantance duk wani abu na rashin da’a da ake tafkawa da wasu masu son zuciya.
Duk da haka, ta ba da tabbacin jajircewar tawagarta ta fasaha da ke aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa atisayen na ranar Laraba ba shi da wata matsala.
Hukumar ta kuma yi wa ’yan Najeriya alkawarin cewa babu wani dan takara da za a hana shi damar yin jarabawar, inda ta ci gaba da cewa, idan aka samu cikas, za a sake sanya irin wannan dan takarar don yin jarabawar a wata rana da wuri ta gaba.
A wani labarin kuma, Shugaban APC na Kasa Adamu, Gbajabiamila Da Wasu Sun Ziyarci Tinubu
Gabanin bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, da shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da sauran shugabannin jam’iyyar da suka hada da kakakin majalisar wakilai, Hon.Femi Gbajabiamila a ranar Talata sun kai masa ziyara.
Sauran wadanda suka ziyarci Tinubu da suka isa kasar a ranar Litinin daga Faransa sun hada da gwamnan jihar Ekiti Biodun Oyebanji, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin.