Kakakin majalisar tarayyar Nijeriya, Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa; shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince ya bayyana gaban ‘yan majalisar domin yi wa ‘yan Nijeriya jawabi akan matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasarnan.
Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan ne a yau Laraba a fadar gwamnatin Villla dake Abuja, a yayin da yake amsa tambayoyin wakilan kafafen watsa labarai na fadar gwamnatin, bayan da ya jagoranci wata tawaga domin ganawa da Buhari.
Kakakin majalisar ya ce sun gana da Buhari ne bayan matsayar da majalisar ta cimma a ranar Talata na bukatar da yake akwai shugaban kasar ya bayyana gabansu kamar yadda membobinsu suka bukata domin yin jawabi akan kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar.
Sai dai ya ce ‘yan majalisar ba su sanya ranar zuwan shugaban kasar ba, domin har yanzu ba su cimma matsayar rana ba. Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba shugaban kasar zai bayyana.