Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu a ranar Litinin din nan a Abuja ya bukaci ma’aikatan kungiyar likitoci masu neman kwarewa da ke yajin aiki da su koma bakin aiki.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Tinubu ya yi alkawarin warware korafe-korafensu a ya yin ganarwa ta su.
“Za mu warware dukkan batutuwan, da fatan za a koma bakin aiki“. Tinubu ya shaida wa shugabannin kungiyar hadin gwiwa ta fannin kiwon lafiya yayin wani taro a fadar gwamnatin.
KARANTA WANNAN Kwararrun Likitocin Koda Ne Kadai Suka Rage A Nigeria
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa kungiyar JOHESU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani mako guda da ya gabata saboda bukatar inganta walwalarsu da sauran bukatu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa kungiyar kwadago ta Nigeria ta ce za ta tsunduma yajin aikin a duk fadin kasar a ranar Laraba nan bayan dakatar da tallafin man fetur.
Shugaban Kasar wanda ya bayyana kudurin gwamnatinsa na farfado da kuma dawo da kwarin gwiwar al’umma a fannin kiwon lafiya ya, ya yi alkawarin warware duk wasu matsalolin da aka gano sun dabaibaye fannin, imya kuma bukaci kungiyar da ke yajin aikin da ta koma bakin aiki.
“Bangaren lafiya yana da matukar muhimmanci ga bil’adama. Za mu warware duk matsalolin”
“Dole ne a sanya amana a duk tattaunawa. Na yi muku alkawarin za mu hanzarta yin wannan. Za mu warware dukkan batutuwan. Don Allah a koma bakin aiki” in ji shugaban Kasa Tinubu ya roki kungiyar.
A yayin da yake bayyana shiri kungiyae na dawo da mambobin bakin aiki, mukaddashin shugaban kungiayar Datka Obinna Ogbonna, ya roki Tinubu da ya mai da hankali kan tsarin samar da kiwon lafiya a Nigeria ta ha yar zuba jari mai kyau a fannin.
A Wani Labarin Kuma Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani Matashi A Gaban Kotu
Rundunar yan sanda a ranar Litinin din nan ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 32 mai suna Bello Isma’il a gaban wata kotyn majistari ta jihaf Ekiti.
Matashin wanda an gurfanar da shi ne bisa zarginsa da karbar wasu shanu na satar.