Rahotanni sun bayyana cewa an hangi ‘yan kungiyar ISWAP suna kafa sansanoni a kusa da kauyen Mutu da ke gundumar Mada na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Shugaban kwamitin hukunta laifukan da suka shafi ‘yan fashi kuma mamba a kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na jiha, Dr Sani Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana hakan a wani taro a Gusau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Dai Na Kaiwa Junan Ku Hare-Hare — INEC Ta Ja Kunnen Jam’iyun Siyasa
Ya ce ‘yan kungiyar ta ISWAP sun kuma shiga jihar ta hanyar Danjibga zuwa Kunchin Kalgo a karamar hukumar Tsafe ta jihar inda ya kara da cewa daruruwan ‘yan bindiga sun razana garuruwa da kauyuka da dama yayin da suke barazanar kai musu hare-hare a ‘yan kwanakin nan.
Ya kara da cewa, “Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, ya yi aiki bisa tsarin doka a lokacin da ya rattaba hannu a kan dokar zartarwa ta 10, ta rufe gidajen yada labarai a jihar. Ya yi aiki ne bisa tsarin doka bisa babi na 2, sashe na 14 da karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dalilan tsaro.
“Ikon zartaswa da na majalisa da na shari’a an bayyana su a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya karara. Don haka matakin da aka dauka shi ne tabbatar da cewa jihar tana cikin kwanciyar hankali sai dai idan ba dan Najeriya ba ne kuma ba ka son fahimtar yanayin lamarin.
“Wannan matakin da gwamnatin jihar ta dauka ya samo asali ne saboda dalilai na tsaro amma ba wai don adawa ba ne kamar yadda wasu ke tunani. Tsaron mutane da dukiyoyi a jihar abu ne mai mahimmanci.
“Mun ga abin da kungiyoyi daban-daban suka ce: NUJ, NBC, IPI kuma mun fahimci damuwarsu amma abin da BON ta ce wani hari ne na kashin kai ga gwamnan jihar. Duk da haka, a madadin gwamnatin jihar muna ba da hakuri kan matakin da muka dauka.”
WANI LABARIN KUMA: Ko Yanzu Yan Najeriya Sun Gamsu Da Ayyukan Raya Kasa Da Muka Samar – Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu ya bude taron karshe na duba kokarin ma’aikatu karkashin gwamnatinsa inda ya ce an gudanar da ayyukan raya kasa wadanda suka gamsar da ‘yan Najeriya.
Yayin da yake jawabi a taron da aka shirya domin auna irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufofi guda 9 na gwamnatinsa, shugaban kasar ya bayyana irin nasarorin da aka samu a fannin noma da tattalin arziki da ayyukan raya kasa da tsaro da lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.