- Mazauna Enugu na fama da ƙarancin ruwa, sun koma amfani da ruwan Leda domin wanka
Wani Mazauni Enugu RAPHEAL EDE ya rubuta akan irin yanayin yadda halin mazauna can yake, biyo bayan ƙarancin ruwa da aka samu a garin duk da rahoton kai ɗauki da aka fitar.
Chukuma Oji wani mazaunin unguwar Ogui kuma malamin makaranta a wasu makarantu a cikin garin Enugu yana zuwa otel da bankuna kullum domin duba irin yanayin ƙarancin ruwa da ke akwai a makwabtan shi, wanda ya sanya baza su iya wanke wajen yin bahayar su.
KARANTA WANNAN LABARIN:Aikin Wannan Gwamnati Ne Kare Nigeria Da Al’ummarta Da Kuma Dimokuradiyya- Garba Shehu
Oji yace yana yin wanka sai ɗaya a cikin kwanaki uku saboda bazai iya kashe Naira ɗari 400 kullum domin sayen jikar ruwa a akan Naira ɗari 200 domin wanka a kullum.
Wannan matsalar ƙarancin ruwa ta zamanto abun da ke cima Jahar Enugu tuwo a ƙwarya musamman a cikin garin a shekaru da dama.
A cewar sa kimanin watanni biyu kenan jahar bata turo ruwa a yankin su, kuma rijiyar da suka dogara dashi da maƙwabtan shi ta ƙafe, sakamakon wannan iftila’i da suke fuskanta.