Daga Mu’azzam Yakubu Sanka Kano
Majiyoyi suna ta kara bayar da haske kan sabanin da ya shiga tsakanin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, da kuma Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda har ta kai ga Gwamnan ya dauki kwakkwaran mataki a kan Sarkin na Kano.
A makon da ya gabata ne, Gwamna Ganduje ya gaggauta sanya hannu a kan dokar nan da ta kirkiro sabbin Masarautu hudu a Jihar ta Kano. Abin da ake ganin tamkar wani hari ne na kai tsaye ga basaraken na Kano.
Baya ga wannan ma, a makon ne, hukumar yin hani da lalata dukiyar al’umma, ta sake bude shafin nan na bincikar yanda Masarautar ta Kano ta kashe kudaden Masarautar, Majalisar Masarautar ta Kano, wacce take tana karkashin Sarki Sanusi ne.
Sai dai kuma, babbar Kotun Kano ta bayar da umurnin dakatar da Gwamna Ganduje daga nada sabbin Sarakunan har sai ta yanke hukunci a kan karar da wasu ‘yan majalisar dokokin Jihar biyu suka shigar a gabanta, inda suke kalubalantar shirin kirkiro sabbin Masarautun hudu.
A bisa la’akari da yanda sakamakon babban zaben da ya gudana na 2019, ana fassara duk wadannan matakan da Gwamna Ganduje yake dauka ne a matsayin tamkar ramuwar gayya a bisa yanda Sarkin na Kano, ya fito fili karara a harkan siyasar ta Kano, yana nuna goyon bayansa ga wani sashe, wanda a karshe kuma Gwamna Ganduje ne ya lashe zaben bayan an maimaita zaben a karo na biyu.
A bisa bayanin fadin yanda gaskiyar lamurran suka gudana, wasu jami’ai da suke kusa da Gwamna Ganduje, sun bayyana mana cewa, a lokacin da aka tsayar da ka’idar za a sake maimaita zaben a wasu sassan Jihar ta Kano, Basaraken na Kano, ya yi zama kimanin sau biyar da shugaban sashen Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma babban abokin hamayyan Gwamna Ganduje, wanda kuma shi ne dan takaran Jam’iyyar PDP a Jihar ta Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda kuma aka fi da kira da, Abba Gida-gida, duk domin tattaunawa a kan yanda za su ci zaben.
Daya daga cikin majiyoyin kuma ta labarta yanda Sarki Sanusi din ya umurci dukkanin Hakiman sa a Jihar ba ma kawai su tabbatar da sun zabi Jam’iyyar ta PDP ba, su ma tabbatar da rashin nasarar Jam’iyyar ta APC a duk Masarautun su. “Ya kuma kira dukkanin danginsa, ya umurce su da su yi wa jam’iyyar PDP aiki, su tabbatar da Gwamna mai ci bai sami nasarar komawa bisa Kujerar sa ba a karo na biyu.
Kamar hakan ma bai wadace shi ba, Sarkin ya yi amfani da duk wata hanya da yake da ita, inda ya tara makudan kudade daga abokanan sa da abokanan kasuwancin sa, domin yakin neman zaben kayar da Jam’iyyar ta APC a lokacin babban zaben,” in ji jami’in. Majiyar Gwamnatin ta kara da zargin cewa, bayan gudanar da zaben gwamnan na 23 ga watan Fabrairu, da kuma shelanta rashin kammaluwar zaben, gwamnan jihar ta Kano, wanda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi, Sarkin ya kirayi wasu manyan mutane masu yawa, yana rokon su da kar su bari a sake maimaita zaben na Kano.
Daga cikin manyan mutanan da ake zargin ya daga waya ya kiraye su, akwai wasu da suke a fadar shugaban kasa, wasu a hukumar zaben ta INEC, da kuma ma wasu daga cikin shugabannin Jam’iyyar ta APC, gami da wasu shugabannin hukumomin tsaro. “Ya shaida ma wasun su cewa, akwai yiwuwar sake barkewar kazamin rikicin siyasa a Kano, matukar dai ba a shelanta dan takaran gwamna a karkashin jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben ba,” in ji majiyar, ta kuma kara da cewa, “A lokacin da ta tabbata za a sake maimaita zaben, sai Sarkin na Kano ya canza takon sa, inda ya nufanci jami’an tsaro ya yi kokarin gamsar da su cewa, su yi aiki wajen ganin faduwar jam’iyyar APC.
An yi zargin cewa, Sarkin ya gana da babban jami’in ‘yan sanda da aka turo domin ya duba yanda zaben zai gudana, ya kuma yi kokarin ya gamsar da shi domin ya marawa dan takaran Jam’iyyar PDP baya, in ji majiyar. Wata kuma majiyar ta gwamnatin Jihar ta Kano, ta zargi Sarki Sanusi, a kan dagewar da ya yi na tabbatar da ganin Ganduje bai sake komowa bisa kujerar gwamnan na Kano ba a karo na biyu, hatta a bayan da gwamnan ya lashe zaben da aka maimaita din, inda a nan ma ya umurci Hakimansa na wuraren da aka maimaita zaben da su rubuto rahotanni marasa dadi a kan zaben da aka maimaita, domin a nuna dai zaben bai yi ba.
“Sarki Sanusi ya umurci dukkanin Hakimansa na wuraren da aka maimiata zaben da su rubuto rahotanni marasa dadi da za su nuna ba zaben gaskiya aka yi ba, su nuna rikici ne ya mamaye zaben. Wasu daga cikin Hakiman na shi sun rubuta abin da ya umurce su da rubutawan, amma wasun su kuma sun ki yin hakan. Hatta wadanda ma suka rubuto rahotanni marasa dadin, daga baya sun bayar da shaida da kansu kan cewa sun yi hakan ne a bisa umurni Sarki Sanusi. Sarkin ya yi abubuwa masu yawa wadanda ba wai sun batawa Gwamna rai ne ba kadai, sun ma shafi baki-dayan Jam’iyyar ta APC ce. ya ma yi zagon kasa a kan zaben shugaban kasa kai tsaye ta hanyar tunzura mutane su ki gwamnatin Buhari,” in ji majiyar.
Majiyoyin na gwamnatin suka yi zargin cewa, duk wadannan abubuwan da Sarki Sanusi ya yi ne suka harzuka Gwamna Ganduje. Gwamnan, a lokacin da aka kawo ma shi sabuwar dokar kirkiro sabbin Masarautu, nan take ya hanzarta sanya hannu a kanta, ya ma garzaya wajen baiwa sabbin Sarakan Sandunan kama aikin su. Wannan kuma, duk kari ne a kan yanda hukumar hana yin facaka da dukiyar al’umma suka gayyaci jami’an Masarautar ta Kano, domin yi masu tambayoyi a kan halin da asusun Masarautar yake ciki.
Wani kuma dalilin na hanzarta kafa dokar kirkiro sabbin Masarautun da Majalisar dokokin Jihar ta Kano ta yi, in ji wasu majiyoyin shi ne, kasantuwar Kakakin majalisar dokokin ta Jihar ta Kano, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum, yana rike ne da Sarautar Turakin Rano, sannan kirkiro Masarautar Rano, zai mayar da shi daya daga cikin masu nadin Sarki a Masarautar ta Rano ne kai tsaye. Turaki yana daga cikin masu zaben Sarki kamar yanda dokar nadin Sarakuna ta Jihar Kano ta tanada, wacce aka yi wa kwaskwarima, 2019.
Wakilinmu kuma ya fahimci cewa, akwai dai mutane da yawa da suke da wasu bukatu na musamman a kan kirkiro sabbin Masarautun daga Karaye da Gaya, daga Masarautar ta Kano.
Ko da wakilin namu ya tuntubi Kwamishinan yada labarai na Jihar ta Kano, Malam Muhammad Garba, cewa ya yi, shi ba zai iya cewa komai ba a kan duk wani abin da ya shafi kirkiro da sabbin Masarautun ko kuma dangantakar da ke tsakanin Gwamnan da Sarkin na Kano, ya yi nuni da cewa, “Ai an rigaya an kirkiro wadannan Masarautun.
Shugaban ma’aiakatan fadar ta Sarki Sanusi, Alhaji Munir Sanusi, ya ki ya ce uffan, yana mai cewa, ba ni da hurumin yin magana da manema labarai a kan wannan maganar, saboda akwai wasu manyan fadawan Masarautar da suke a samana.