Dan wasan Faransa da Paris St. Germain Kylian Mbappe ya ce a kowane wayewan garin Allah Yana zaunar da kan shi ya faɗa wa zuciyar shi cewa yana gaba da Lionel Messi da Christiano Ronaldo.
Magoya bayan kwallon kafa na ci gaba da hasashe cewa Mbappe ka iya jan zaren sa da zarar Messi da Ronaldo sun shude daga fagen kwallon kafa.
Kamar yadda Mbappe mai shekara 22 yake faɗa, jin kan shi a sama da Ronaldo da Messi wata dama ce t kara wa kai kwarin gwiwa, kuma haka na da matukar alfanu muddin mutum son taka wani tsani.
“Izza? Yana da muhimmanci sosai, saboda idan kana cikin Wani yanayi babu wanda zai zakuɗa ka sai dai kai da kan ka” Cewar Mbappe.
“To ka ga dole ne ka ji a ran ka cewa za ka iya taka ko wane irin tsani na rayuwa”
“Mutane ba su fahimci menene aje nufi da izza ba, Idan fa ba ka da lafiya, babu wanda zai zo gidan ka ya gaya maa abin da za ka yi, kai da kai kan ka za ka yi abin da ya dace da kai, saboda haka dole ka ji a ran ka sa ka iya yin abubuwan bajinta”.
A yanzu haka Mbappe ya samu nasarar lashe kofuna goma na cikin gida ciki har da kofin ligue 1 na ƙasar Faransa yauin da kuma ya zura kwallaye dai-dai har 150 a dukkannin wasan da ya fafata wa Ƙungiyar”.
Kazalika ya lashe kofin duniya ta World Cup, to sai dai Messi da Ronaldo sun ci gaba da kasafta Kyuatar gwarzon kwallon kafa ta duniya ta Ballon d’Or a tsakanin su har gusa goma sha ɗaya.