Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata ‘yar kasuwa mai suna Maria Yakubu, a ranar Juma’a ta kai mijinta Gana Yakubu zuwa wata kotun gargajiya da ke zaune a Nyanya bisa zarginsa da sanya mata laya a kan gadonta.
Mai shigar da karar ta fadi haka ne a cikin karar da ta shigar a gaban kotu game da neman aka she auren dake tsakanin ta da mijin nata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Watsi Da Faifan Bidiyo Da Ke Nuna Harin Da Aka Kai A Ofishin Kwastam Na Yola
“Tun da muka gama gina sabon gidanmu muka koma, ni da mijina muka fara samun rashin fahimtar juna, duk lokacin da na dawo gida, matsala daya ce ko daya yau she.
“Wani lokaci mijina zai dawo gida da wata mace. Don kawai in fusata, ban taba mayar da martani ba, ba abu ne mai sauki ba amma na yi ta kokarin kada in mayar da martani.”
“A wata rana mai aminci, na dawo gida na shiga dakina, na ga layoyi a kan gadona, na fuskanci mijina da maganar sai ya musanta, sai na kai maganar zuwa wajen ‘yan sanda. Daga baya mijina ya furta cewa shi ne ya sanya layoyin.”
Mai shigar da karar ta kara rokon kotun data datse igiyar auren ta da mijin nata, tana mai cewa: “Bana son in mutu ta dalilin yin wannan auren.”
Sai dai alkalin kotun, Shitta Abdullahi, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 8 ga watan Agusta domin mijin ya kare kan shi.
A Wani labarin Kuma Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire (STI), Dr Adeleke Mamora ya ce gwamnatin tarayya za ta magance yanayin aikin ma’aikatan lafiya a Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar kungiyar likitocin Najeriya (NMA) karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Dr Uche Ojinmah suka kai masa ziyara a Abuja ranar Alhamis din nan.
Mamora ya ce gwamnati za ta yi kokarin inganta yanayin aiki da kuma biyan albashin ma’aikatan lafiya, musamman ma likitoci.
Ya ce tilas ne a daina fita da ma’aikatan lafiya, musamman likitoci zuwa kasashen ketare.
A cewarsa, gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don dakile halin da likitocin ke ciki da suke tafiya ketare.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mamora ya yi alkawarin kare muradun likitoci da ma’aikatan lafiya, la’akari da dabarunsu ga bil’adama.
Ya kuma bukaci kungiyar da ta ci gaba da rike amana da kuma gudanar da aiki daidai da rantsuwar kama aikinsu.
Tun da farko, Dokta Ojinmah, shugaban kungiyar NMA, ya bukaci ministan da ya tattauna wasu kalubalen kungiyar kamar yanayin aiki, kayan aiki da kuma albashi a taron majalisar zartaswa ta tarayya FEC a madadinsu.
(NAN)