Ministan lafiya a kasar Ajantina Gonzalez Garcia, ya ajiye aiki bayan da shugaban kasar Alberto Fernandez ya umarce shi da yin haka bayan yi wa abokansa alfarmar allurar rigakafin corona.
Rikicin ya yi kamari ne bayan da wani dan jarida mai shekaru 71 ya sanar a rediyo cewa ya samu allurar a ofishin ministan gabannin a fara yi wa al’ummar kasa saboda dadadden abotar da ke tsakaninsu.
Wasu kafafen yada labarun Ajantina sun ruwaito ‘yan uwa da abokan ma’aikatan gwamnati, sun samu allurar a ma’aikatar lafiya gabannin a fara yin allurar a hukumance a ranar Laraba mai zuwa.