Babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika, inda ya bayyana matsalolin shigar da zaben fidda-gwani na kai tsaye a cikin kudirin gyara dokar zabe.
An tattaro a ranar Alhamis, cewa shugaban kasa ya karbi wasikar babban lauyan kan dokar zaben da aka yi wa kwaskwarima makonni biyu da suka gabata.
Da jaridar The Punch ta tuntuba ta wayar tarho, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa shugaban kasar ya samu sako daga Malami kan kudirin.
Sai dai ya ce bai da masaniya kan abun da wasikar ta kunsa.
“ Zan iya tabbatar da cewa shugaban kasa ya samu sako daga mai girma minista kan lamarin amma a gaskiya ban san abin da ya kunsa ba. Ba a yi mini bayani ba,” in ji mai taimaka wa shugaban kasar.
Sai dai wata majiya a ma’aikatar shari’a ta shaida wa daya daga cikin ‘yan jaridu cewa Malami ya sanar da shugaban kasar cewa sanya wa dukkan jam’iyyun siyasa tikitin takara kai tsaye zai iya haifar da rudani.
Wata majiya mai tushe a ma’aikatar ta ce, “babban lauyan gwamnatin tarayya ya aike da shawararsa kan kudirin gyaran dokar zabe ga shugaban kasa. Ya bayyana matsalolin kudirin.
“Lauyan, ba ta kawo wani sashe na dokar da ta haramta hakan ba, sabanin wasikun da ya rubuta wa shugaban kasa a baya.”
Haka kuma, wata majiya a ofishin AGF ta tabbatarwa da jaridar PUNCH cewa lallai Malami ya rubutawa shugaban kasa.
Ya yi bayanin cewa ya damu matuka cewa tilasta wa dukkan jam’iyyu yin tsarin zaben fidda gwanin kai tsaye zai sa duk jam’iyyun da ake da su su canza kundin tsarin mulkin su.
Majiyar ta bayyana cewa, “Ofishin babban lauyan ya aika da matsayarsa makonni biyu da suka gabata. Sun tabo batutuwa da dama. Misali, idan kuna neman jam’iyyun siyasa su gudanar da zabukan fidda-gwani kai tsaye, ta mahangar shari’a wanda hakan na nufin cewa sabbin jam’iyyun siyasa ne kawai za su kasance masu bin doka.
“Jam’iyyun siyasa da ake da su ba za su yi ba, saboda sun yi rajistar jam’iyyunsu, sun riga sun shigar da kundin tsarin mulkin su tun da dadewa a kan abin da ya kunsa. Kuma mafi yawansu cakude ne, idan ka duba jam’iyyu, an bayyana zaben fidda gwani kai tsaye da kaikaice.
“To, za ku canza musu kundin tsarin mulkinsu? Don haka, wannan shine ra’ayin shari’a. Amma wannan daya ne kawai. Akwai wasu mukamai da dama na shari’a wadanda suka nuna goyon baya da rashin amincewa da kudirin saboda a matsayinsa na Ministan Shari’a, aikinsa shi ne ya gaya wa shugaban kasa alheri da rashinsa. Yanzu ya rage ga Shugaban kasa ya yanke shawarar hanyar da zai bi.”
Da aka tuntubi Kakakin Malami, Dakta Umar Gwandu, ya ce ba shi da hurumin tabbatar da faruwar lamarin.
“Mai girma babban lauyan gwamnati na tarayya kuma Ministan Shari’a yana halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na 2021 na Jam’iyyun Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ake gudanarwa a Masar a halin yanzu.
“Ba ni da ikon tabbatar da ko wani ra’ayi ya fito daga babban mai shari’a na tarayya kuma ministan shari’a game da dokar gyara dokar zabe. Ba zan iya tantance sahihancin da’awarku ba a halin yanzu.”
Kungiyoyin kare hakkin jama’a da dama sun yi ta matsin lamba ga shugaban kasa kan ya rattaba hannu kan kudirin musamman domin ya baiwa hujumar INEC ikon mika sakamakon zabe ta hanyar intanet.
Har ila yau, wasu sun yi iƙirarin cewa zaɓen fidda gwani na tilas ne zai samar da daidaito tsakanin mata da matasa.
Sai dai gwamnonin jam’iyyar APC sun fito fili suna adawa da zaben fidda gwani na tilas da suka hada da Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi.