Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce har yanzu Nijeriya na bukatar kwarewa da shawarar hafsoshin sojan da suka yi ritaya wajen tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.
Matawalle ya bayyana haka ne a wani liyafar cin abincin dare na karrama babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, wanda mambobin kungiyar makarantar soji ta kasa (NDA) 38 Regular Course Welfare Association suka shirya ranar Asabar a Abuja.
Ya kara da cewa al’ummar kasar na bukatar su a matsayin kwararru da za su zo don amfani da kwarewarsu da gogewarsu wajen samar da mafita ga dimbin kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.
A cewarsa, ana sa ran a yanzu sun samu lokaci na musamman domin tunowa da kuma gabatar da ra’ayoyin da za su magance matsalolin ba tare da wata tangarda ba.
Karanta nanRigakafin Cutar Kansa Bashida Illa Ku Bari Ayiwa ‘Ya’Yanku-Zainab Bagudu Ga ‘Yan Nijeriya
Ina so in tabbatar muku cewa ma’aikatar tsaro a shirye take ta karbe ku a matsayin kungiyar kwararrun masana don tattaunawa kan batutuwan tsaro a kasarmu.
Saboda dimbin horo da gogewar wadannan fitattun mutane da kwararrun jami’an tsaro za mu tabbatar da cewa munci gaba da daukar nauyin ku a matsayin mashawartanmu a ma’aikatar tsaro inji shi.
A wani labarin kumaMu Hadu A Kotun Koli-Jam’iyar APC A Jahar Adamawa Ta Fadawa Fintiri
Ministan ya ce kokarin ciyar da kasa gaba wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, inda ya ce tuni Allah ya albarkaci Najeriya da manyan hafsoshi na soja.
Ya yabawa kungiyar bisa karrama dan kungiyarsu da aka nada a matsayin hafsan tsaro da kuma kokarin da suke yi na kyautata rayuwar ‘yan uwa da sauran al’umma baki daya.