Ministoci: Majalisar Dattawa za ta sake gayyatar El-Rufai Da Wasu Mutum Biyu
Kakakin majalisar Dattijai, Yemi Adaramodu ya ce mai yiwuwa su sake gayyato sunayen mutane uku na ministoci da ba a tabbatar da su ba don sake tantance su.
Adaramodu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels.
KARANTA WANNAN LABARIN:CBN Ya Bayyana Manufofi Da Fa’idojin Amfani Da Tsarin e-Naira
Majalisar ta ki amincewa da tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dan takarar jihar Delta, Stella Okotete da kuma na jihar Taraba, Abubakar Danladi, bisa dalilan tsaro.
Da aka tambaye shi ko har yanzu majalisar dattawa za ta tabbatar da su, Adaramodu ya mayar da martani: “Tambayar da aka yi a kansu batu ne da ke gudana.
“Don haka, da zarar Majalisar Dattawa ta gamsu, tabbas, idan muna bukatar gayyatar su zauren majalisa don sake tantancewa da sake tantance su, to za mu yi hakan.
“Idan ba a gamsu da tsaro ba, Majalisar aaaDattawa ba za ta iya gamsuwa ba. Ya danganta da abin da hukumomin tsaro da wanda ya nada su ya ce.”
A ranar litinin ne majalisar dattawa ta amince tare da tabbatar da sunayen ministoci 45 da shugaba Bola Tinubu ya turawa majalisar.
Sai dai ‘yan majalisar sun ki amincewa da El-Rufai da wasu mutane biyu minista har sai an sami “kwancen tsaro.
A wani labarin kuma:Najeriya ta yi asarar dala biliyan 7 sakamakon ambaliyar ruwa a shekarar 2022 – FG
Gwamnatin tarayya ta ce barnar da aka samu a kasar sakamakon ambaliyar ruwa a shekarar 2022 ya kai kimanin dala biliyan 7.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a Abuja ranar Talata.