- Makarantu da dama suna da ɗalibai sama da 250 wanda malami ɗaya ne kawai a aji yake koyar dasu
- Malamai 24 suna koyar da dalibai 1,726 a Makarantar dake karamar hukumar Misau
- An shigar da yaran da ba su zuwa makaranta su 37 ciki aji
A kalla makarantu 79 a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi suna da malami daya ne kowannen su ke koyar da dukkan darussa ga dalibai, kamar yadda The Punch ta rawaito.
Darakta mai kula da ayyukan makarantu na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Bauchi, Korijo Usman ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani taron tattaunawa da asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya shirya kan shirin daukar yaran da ba sa zuwa makaranta a kananan hukumomin Misau da Alkaleri.
KARANTA WANNAN: An Ankarar da Jami’an Kwastam Da Ke Kan Bodar Najeriya da Wasu Ƙasashe
Da yake jawabi a makarantar central firamare dake karamar hukumar Misau, Usman ya ce yawancin makarantu a karamar hukumar da kuma fadin jihar ba su da isassun malaman da za su koyar da yaran.
“A Misau akwai makarantu 79 da kowannensu ke da malami daya yayin da babu malamai, Duk makarantun suna da malamai sai dai ba su isa ba.
“Karamar hukumar Misau ta fi kyau idan aka kwatanta da sauran. Ku je wasu makarantu ku ga halin da ake ciki. Don haka abin da za mu yi shi ne mu gano inda suke da cunkoso sai mu ce su sake tura su wasu malaman zuwa wuraren da basu isa ba.
“Kuma shi ne abin da muka gaya musu daga SUBEB cewa idan sun ga makarantar da malamai da yawa su koma wasu makarantu biyu ko uku gwargwadon adadinsu.
“A nan makarantar (Misau Central Firamare), suna da dalibai 1,726 da malamai 24. Idan ka yi lissafin za ka ga cewa mafi karancin ma’aunin malami da na dalibi shi ne 45 kuma za ka ga ba mu da shi a Najeriya. A wannan makaranta, akwai rabon malamai 72 kowane aji.
“Idan ka je babban birnin Bauchi, za ka ga akwai ajujuwa 150 ko 200, har ma da dalibai 220 zuwa 250 da malami daya kacal. Don haka nasu a nan ya fi kyau saboda za ka ga suna da 72 a aji, nasu ya fi idan aka kwatanta da karamar hukumar Bauchi.
“Akwai wasu makarantun da daliban ma ba su kai 1,000 ba amma suna da malamai sama da 30 kuma yawancinsu mata ne,” inji shi.
Da yake jawabi tun da farko, Sakataren Ilimi na Hukumar ta Misau, Alhaji Abdu, da aka tambaye shi game da rashin isassun malamai a makarantar, ya ce halin da ake ciki a makarantar firamare ta Misau ta fi sauran makarantun karamar hukumar kyau.
Ya ce “Malaman da muke da su a nan makarantar, haka muke sarrafa su. Zan iya gaya muku cewa wannan makaranta daya ce daga cikin makarantun da ke da malamai da yawa, muna da wasu makarantu da ke da dalibai sama da 600 masu malamai bakwai kacal.
“Ina gaya muku cewa idan kun je wasu makarantu, za ku yi mamaki sosai. A wannan makaranta muna da isassun malamai idan aka kwatanta da sauran da yawa a nan karamar hukumar Misau. Abin da muke yi shi ne mu hada kai da SBMC don ganin muna da malamai ‘yan sa kai.”
Da aka tambayi Umar ko me suke yi don magance wannan samar da isassun ma’aikata a makarantar da sauran su a fadin jihar, Daraktan Kula da Makarantun Korijo Umar ya ce “SUBEB ba ta daukar malamai aiki.”
“Abin da muke yi shi ne tura malamai kawai a makarantu. Hukumar kula da ayyukan malamai ta dora alhakin daukar malamai aiki tare da hadin gwiwar SUBEB.
“Mu, SUBEB, muna aiki a matsayin masu kulawa. Bayan haka (aiki na malamai),shine sai su buga mana sunayen sannan mu tantance su.
“Idan suka ba mu sunayen, za mu tantance su don ganin wadanda suka yi tsalle ta taga, watakila takardar shaidar karatun ba daidai ba ce, ko kuma ba takardar shaidarsa ba ce ko wasu dalilai. Daga nan sai mu cire sunayen, mu ce su musanya sunayen da sauran ma’aikata,” ya kara da cewa.
A halin da ake ciki dai, dalibai 37, wadanda suka kunshi maza 20 da mata 17, wadanda ba sa zuwa makaranta, an shigar da su makarantar firamare ta tsakiya da ke Misau, bayan bullo da wani sabon tsari mai suna “Teaching at the Right Level” SUBEB da UNICEF.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda: Wani Mutum Da Aka Gani Da Gawar Yaro Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Jami’an ‘yan sanda daga sashin Ilemba-Hausa na rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun shiga tsakani a kan lokaci, sun ceto wani mutum da aka samu da gawar yaron abokinsa.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN faruwar lamarin a ranar Lahadin nan.