Mu haɗu mu tallafawa Talakawa da marasa galihu, Adeleke ya kirayi masu Hannu da Shuni
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ƙalubalanci masu hannu da shuni a Jihar da su yi koyi da ‘yar uwarsa wajen tallafa wa talakawa da marasa galihu a cikin al’umma.
Da yake Jawabi a wajen Taron wayar da kan Jama’a da gidauniyar Yeye Dupe Adeleke Sanni ta shirya a gidan Ede a ranar Juma’a, ya jaddada buƙatar masu hannu da shuni da su marawa Gwamnati baya wajen tallafa wa talakawa domin ganin al’umma ta samu yanayi mai kyau ga kowa da kowa.
A cewar Gwamnan, ayyukan taimakon Jama’a da Gidauniyar keyi musamman a Jihar, yana sa al’umma su samu chanjin yanayi cikin sauri don haka yana kira ga wasu da su yi koyi da Adeleke na bayar da tallafi ga mabuƙata.
“Na yi farin cikin haɗuwa da ‘yar uwata da Mahaifiyata yayin da take ci gaba da aiwatar da ayyukan da ke jaddada al’adar iyalin gidansu, Wannan abin a yaba ne kwarai da gaske, duk da na san cewa wannan ƙoƙarin ya kamata ya zama cikin sirri. Amma wajibi ne ga masu hannu da Shuni da su tallafawa Talakawa da marasa galihu.
KARANTA NAN:Ku Tabbatar Anyi Sahihin Zabe A Jahohin Imo,Bayelsa Da Kogi-Tinubu Ga INEC
“Al’umma na haɓaka da kuma samun cigaba mafi kyau idan ya kasance muna son maƙwabtanmu kamar yadda muke son kanmu, Wannan ita ce al’adar gidanmu, kuma ina farin ciki ‘yar’uwata ta riƙe wannan cikin gaskiya” in ji shi.
Da take Jawabi wacce ta kafa gidauniyar wacce kuma ita ce kanwar Gwamna, Mrs Dupe Adeleke Sanni ta buƙaci waɗanda suka amfana da kada su sayar da kayayyakin tallafin da aka ba su, sai dai su yi amfani da shi domin amfanin iyalansu.
Ta nanata cewa karfafawa mata ne a faɗin ƙananan hukumomi talatin da Ofishin yankin da ke Jihar, inda ta ƙara da cewa burinta shine ta sa su zamo masu dogaro da kansu.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da ƙananan motocin bas guda 50, da manyan Firizoji guda 100, sai injin niƙa da Ɗinki guda 50, da injin busar gashi guda 10 ga mata da aka zaɓo a faɗin Jihar, inda ta ƙara da cewar Wannan ba shine na ƙarshe ba, domin sauran Jama’a za su ci gajiyar tallafin a wani zagaye na gaba.