Ziyarar kwana biyu da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya Kai a Mali ta zo karshe batare da cimma wata yarjejeniyar ba, kan sanya ranar gudanar da zaben kasar, domin dawowar Mulkin farar hula.
Mr Jonathan wanda ke shiga tsakanin Mali da Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika watau ECOWAS, ya je kasar ne domin sanya ranar zabe, bayan gwamnatin Mulkin sojin kasar ta Mali ta ce sai nan da shekaru biyar kafin ta mika mulki ga farar hula, wa’adin da ECOWAS ke ganin yayi mata nisa.
Idan za’a iya tunawa dai, Sojin Mali sun kwace iko ne da kasar tun a shekarar 2020, lamarin da ya sanya kungiyar ECOWAS ta sanyawa ƙasar wasu takunkumi bayan fatali da gudurin gudanar da zabe a kasar cikin watan Fabrairun shekarar nan.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Tunisia ta sanar da cewa, wani karo da aka yi tsakanin wasu jiragen kasa biyu na fasinja sun raunata akalla mutane 95 a ranar Litinin a kudancin babban birnin Tunisiya.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci kuma ba a samu mace-mace ba,” in ji mai magana da yawun hukumar tsaro ta farar hula, Moez Triaa, ya shaidawa manema labarai, inda ya kara da cewa daya daga cikin jiragen kasan na dauke da fasinjoji.
Ya ce akasarin mutanen da hatsarin ya rutsa dasu sun samu raunuka da karaya, amma babu daya daga cikinsu da ke fuskantar barazana ga rayuwa.
An ce fasinjoji da dama sun shiga cikin firgici, kuma an aike da motocin daukar marasa lafiya kusan 15 domin yi wa wadanda suka jikkata magani da kuma kai su asibiti.
Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 9:30 na safe agogon kasar a yankin Jbel Jelloud, kan hanyar da ta tashi a tsakiyar birnin Tunis.
Wani dan jarida a wurin yace yaga an gogi gaban daya daga cikin jiragen.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin faruwar hatsarin ba, kuma kamfanin jiragen kasa na kasar bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba.
Ministan Sufuri, Rabi Majidi, ya ziyarci inda hatsarin ya afku amma bai yi magana da manema labarai ba.
Tsarin layin dogo na kasar Tunusiya ya gamu da hatsari da dama a cikin ‘yan shekarun nan.
Tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, kasar ta ga hatsarin jirgin kasa 173 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 229 da raunata 345, a cewar mai magana da yawun hukumar hana afkuwar hadurran sufuri, Achraf Yehyaoui.
Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu fiye da 50 suka jikkata a karshen shekarar 2016 lokacin da wani jirgin kasa ya afkawa wata motar safa da ke kusa da wurin da hatsarin ya faru a ranar Litinin.
Wani jami’i ya ce sigina da kofofin tsaro sun daina aiki a lokacin da hadarin ya afku.
A shekarar da ta gabata, kasar da ke arewacin Afirka ta fuskanci daya daga cikin bala’o’in layin dogo mafi muni, inda mutane 18 suka mutu a lokacin da wani jirgin kasa ya afkawa wata babbar mota tare da karkatar da titin a wani matakin tsallaka kudu a babban birnin kasar, sakamakon gazawar da aka samu.
Kasar da ke da kasa da mutane miliyan 12 ita ma tana da mummunan yanayin kiyaye hanyoyin mota, inda wasu mutane 980 suka mutu yayin da sama da 6,500 suka jikkata a bara, a cewar ma’aikatar cikin gidan kasar.